1
M.Had 8:15
Littafi Mai Tsarki
HAU
Abin da na ce, shi ne mutum ya ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne ya ci, ya sha, ya ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakinsa wanda Allah ya ba shi a wannan duniya.
Compare
Explore M.Had 8:15
2
M.Had 8:12
Ko da yake mugun mutum ya aikata laifofi sau ɗari, amma kuwa ya rayu, duk da haka na sani idan kana tsoron Allah kome zai tafi daidai.
Explore M.Had 8:12
3
M.Had 8:6
Akwai lokacin da ya dace, da hanyar da ta dace na yin kowane abu, ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa.
Explore M.Had 8:6
4
M.Had 8:8
Ba wanda zai iya hana kansa mutuwa, ko ya dakatar da ranar mutuwarsa. Idan yaƙi ya zo ba makawa, ba yadda za mu yi mu zurare.
Explore M.Had 8:8
5
M.Had 8:11
Don me mutane suke aikata laifofi a natse? Domin ba a hukunta laifofi nan da nan.
Explore M.Had 8:11
6
M.Had 8:14
Dubi aikin banza da yake faruwa a duniya. Wani lokaci adalai suke shan hukuncin da za a yi wa mugaye, mugaye kuwa su karɓi sakayyar da za a ba adalai. Na ce wannan ma aikin banza ne.
Explore M.Had 8:14
7
M.Had 8:7
Ko ɗaya daga cikinmu ba wanda ya san abin da zai faru, wane ne zai faɗa mana?
Explore M.Had 8:7
Home
Bible
Plans
Videos