1
M.Had 3:1
Littafi Mai Tsarki
HAU
Dukan abin da yake faruwa a duniyan nan yakan faru ne a cikin lokacin da Allah ya so.
Compare
Explore M.Had 3:1
2
M.Had 3:2-3
Shi yake sa lokacin haihuwa, da lokacin mutuwa, Da lokacin dashe, da lokacin tumɓuke abin da aka dasa, Da lokacin kisa, da lokacin rayarwa, Da lokacin rushewa, da lokacin ginawa.
Explore M.Had 3:2-3
3
M.Had 3:4-5
Shi ne kuma yake sa lokacin yin kuka, da lokacin yin dariya, Da lokacin yin makoki, da lokacin yin murna, Da lokacin warwatsa duwatsu, da lokacin tattarawa, Da lokacin rungumewa, da lokacin da ba a yi.
Explore M.Had 3:4-5
4
M.Had 3:7-8
Da lokacin ketawa, da lokacin gyarawa, Da lokacin yin shiru, da lokacin magana. Shi ne kuma yake sa lokacin ƙauna, da lokacin ƙiyayya, Da lokacin yaƙi, da lokacin salama.
Explore M.Had 3:7-8
5
M.Had 3:6
Shi ne kuma yake sa lokacin nema, da lokacin rashi, Da lokacin adanawa, da lokacin zubarwa
Explore M.Had 3:6
6
M.Had 3:14
Na sani dukan abin da Allah ya yi zai dawwama, ba abin da za a ƙara, ko a rage. Allah ya yi haka kuwa domin mutane su zama masu tsoronsa.
Explore M.Had 3:14
7
M.Had 3:17
Sai na ce a zuciyata, “Da adali, da mugu, Allah zai shara'anta su, domin an ƙayyade lokaci na yin kowane abu da na yin kowane aiki.”
Explore M.Had 3:17
Home
Bible
Plans
Videos