1
M.Had 2:26
Littafi Mai Tsarki
HAU
Allah ne yake ba da hikima, da ilimi, da farin ciki ga wanda yake ƙauna. Amma yakan sa matalauci, mai zunubi, ya yi ta wahalar nema ya tara dukiya, domin Allah ya bayar ga wanda yake ƙauna. Wannan ma aikin banza ne, harbin iska ne kawai.
Compare
Explore M.Had 2:26
2
M.Had 2:24-25
Ba abin da ya fi wa mutum kyau fiye da ya ci, ya sha, ya saki jiki, ya ci moriyar aikinsa. Na gane wannan ma daga wurin Allah ne. Ƙaƙa za ka sami abin da za ka ci, ko ka ji daɗin zamanka in ba tare da shi ba?
Explore M.Had 2:24-25
3
M.Had 2:11
Na yi tunani a kan dukan abin da na aikata, da irin wahalar da na sha lokacin da nake yin aikin, sai na gane ba shi da wata ma'ana, na zama kamar mai harbin iska, ba shi da wani amfani.
Explore M.Had 2:11
4
M.Had 2:10
Duk abin da nake so, na samu, ban taɓa hana wa kaina kowane irin nishaɗin da nake so ba. Ina fariya da kowane irin abin da na aikata. Wannan shi ne ladana na dukan aikina.
Explore M.Had 2:10
5
M.Had 2:13
To, na sani hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu.
Explore M.Had 2:13
6
M.Had 2:14
Mai hikima ya san inda ya nufa, amma wawa ba zai iya sani ba. Na kuma sani makomarsu guda ce.
Explore M.Had 2:14
7
M.Had 2:21
Kai ne ka yi aiki da dukan hikimarka, da iliminka, da gwanintarka, amma kuma tilas ka bar shi duka ga wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma bai amfana kome ba, mugun abu ne.
Explore M.Had 2:21
Home
Bible
Plans
Videos