Ga shi, zan sanar da ku wani asiri! Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, amma dukanmu za a sauya kamanninmu, farat ɗaya da ƙyiftawar ido, da jin busar ƙaho na ƙarshe, domin za a busa ƙaho, za a kuma ta da matattu da halin rashin ruɓa, za a kuma sauya kamanninmu.