1
Mattiyu 15:18-19
Sabon Rai Don Kowa 2020
SRK
Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.
Compare
Explore Mattiyu 15:18-19
2
Mattiyu 15:11
Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”
Explore Mattiyu 15:11
3
Mattiyu 15:8-9
“ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”
Explore Mattiyu 15:8-9
4
Mattiyu 15:28
Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take.
Explore Mattiyu 15:28
5
Mattiyu 15:25-27
Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!” Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.” Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.”
Explore Mattiyu 15:25-27
Home
Bible
Plans
Videos