L.Fir 11
11
Dabbobin da yake Halal da na Haram
(M.Sh 14.3-21)
1Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi 2domin Isra'ilawa. Za ku ci kowace irin dabbar da take a duniya, 3wadda take da rababben kofato, wadda kuma take yin tuƙa. 4Ko daga cikin masu tuƙar ko masu rababben kofaton ba za ku ci waɗannan ba. Raƙumi yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku. 5Rema tana tuƙa, amma ba ta da rababben kofato, haram ce a gare ku. 6Zomo yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku. 7Alade yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, haram ne a gare ku. 8Ba za ku ci namansu ba, ba kuwa za ku taɓa mushensu ba, gama haram ne a gare ku.
9Kwa iya cin waɗannan abubuwan da suke cikin ruwa, kowane abin da yake da ƙege da kamɓorin da yake cikin tekuna ko koguna. 10Amma kowace irin halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, abar ƙyama ce a gare ku. 11Namansu kuma zai zama abin ƙyama a gare ku, ba za ku ci ba. Mushensu kuma abin ƙyama ne. 12Kowane irin abin da yake cikin ruwa da ba shi da ƙege da kamɓori, abin ƙyama ne a gare ku.
13Za ku ji ƙyamar waɗannan irin tsuntsaye, ba za ku ci su ba, gama abin ƙyama ne su, wato, gaggafa, da mikiya, da ungulun kwakwa, 14da shirwa, da buga zabi, da irinsu, 15da kowane irin hankaka, 16da jimina, da mujiya, da shaho, da irinsu, 17da ƙururu, da babba da jaka, da zarɓe, 18da kazar ruwa, da kwasakwasa, da ungulu, 19da shamuwa, da jinjimi da irinsa, da burtu, da jemage.
20Dukan ƙwarin da yake da fikafikai ƙazantattu ne, 21sai dai waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle. 22Za ku iya cin fara, da gyare, da ƙwanso da irinsu. 23Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, sun a kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.
24Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har faɗuwar rana. 25Duk wanda kuma ya ɗauki mushensu dole ne ya wanke tufafinsa, amma zai ƙazantu har zuwa maraice. 26Kowace dabba wadda ba ta da rababben kofato, ba ta kuma tuƙa, haram ce a gare ku. Duk wanda ya taɓa su zai ƙazantu. 27Duk abin da yake tafiya a kan daginsa daga cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa maraice. 28Wanda kuma ya ɗauki mushensu, sai ya wanke tufafinsa, ya zama ƙazantacce har zuwa maraice.
29Waɗannan ƙananan dabbobin da suke rarrafe a ƙasa haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa, 30da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo. 31Duk wanda ya taɓa su ko ya taɓa mushensu, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice. 32Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice, sa'an nan zai tsarkaka. 33Idan wani daga cikinsu ya fāɗa cikin kasko, to, kaskon da abin da yake cikinsa za su ƙazantu, sai a fasa kaskon. 34Kowane irin abincin da yake cikinsa kuma da yake da ruwa a cikinsa, zai haramtu. Kowane irin abin sha da yake cikinsa kuma, zai haramtu. 35Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai, zai haramtu, ko randa ce, ko murhu, sai a farfasa, sun ƙazantu, haram ne a gare ku. 36Duk da haka maɓuɓɓuga, ko tafkin ruwa ba za su haramtu ba, amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu. 37Idan kuma kowane ɓangare na mushen ya fāɗa a kan kowane iri da za a shuka, ba zai haramta shi ba. 38Amma idan an zuba ruwa a kan irin, mushen kuwa ya fāɗa kan irin, zai haramta a gare ku.
39Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice. 40Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice.
41Ba za ku ci ƙananan dabbobin da suke motsi a bisa ƙasa ba, 42duk waɗanda suke jan ciki, da waɗanda suke da ƙafa huɗu, da waɗanda suke da ƙafafu da yawa. 43Kada ku ƙazantar da kanku da cin waɗannan abubuwa. 44#L.Fir 19.2; 1Bit 1.16 Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne. 45Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne.
46Wannan ita ce dokar da ta shafi kowace dabba, da kowane tsuntsu, da kowace irin halitta wadda take tafiya cikin ruwa da kowace irin halitta da take a tudu. 47Dole ku lura ku bambanta tsakanin masu tsarki, da marasa tsarki, da tsakanin dabbobin da za a ci, da waɗanda ba za a ci ba.
Đang chọn:
L.Fir 11: HAU
Tô màu
Sao chép
So sánh
Chia sẻ
Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập
@Bible Society of Nigeria 1979

: