L.Fir 12
12
Tsarkakewar Mata bayan Haihuwa
1Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan domin jama'ar Isra'ila. 2Idan mace ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, to, za ta zama marar tsarki har kwana bakwai, kamar cikin kwanakin hailarta. 3#Far 17.12; Luk 2.21 A kan rana ta takwas za a yi wa jaririn kaciya. 4Sa'an nan kuma sai ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana talatin da uku. A lokacin ba za ta taɓa kowane tsattsarkan abu ba, ba za ta shiga wurin yin sujada ba, har kwanakin tsarkakewarta su cika. 5Amma idan 'ya mace ce ta haifa, za ta zama marar tsarki mako biyu kamar a kwanakin hailarta. Za ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana sittin da shida.
6Sa'ad da kwanakin tsarkakewarta na haihuwar ɗa ko 'ya suka cika, sai ta kai wa firist ɗan rago bana ɗaya, a ƙofar alfarwa ta sujada don hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara, ko kurciya na yin hadaya don zunubi. 7Sai ya miƙa ga Ubangiji, ya yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka. Wannan shi ne abin da ya wajaba ga wanda ta haifi ɗa ko 'ya.
8 #
Luk 2.24
Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.
Đang chọn:
L.Fir 12: HAU
Tô màu
Sao chép
So sánh
Chia sẻ
Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập
@Bible Society of Nigeria 1979

: