Fit 28
28
Tufafin Firistoci
1“Daga cikin 'ya'ya maza na Isra'ila sai ka kirawo ɗan'uwanka Haruna tare da 'ya'yansa, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar, su zama firistoci masu yi mini aiki. 2A ɗinka wa Haruna ɗan'uwanka, tufafi masu tsarki domin daraja da kwarjini. 3Ka kuma yi magana da gwanayen sana'a duka waɗanda na ba su fasaha, don su ɗinka wa Haruna tufafi, gama za a keɓe shi ya zama firist ɗina. 4Waɗannan su ne irin tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da falmaran, da taguwa, da zilaika, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan'uwanka, Haruna, da 'ya'yansa tufafi tsarkaka, don su zama firistoci masu yi mini aiki. 5Sai su yi amfani da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.
6“Za su yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya da mulufi, da lallausan zaren lilin, aikin gwani. 7Za a yi mata kafaɗa biyu, sa'an nan a haɗa su a karbunsu. 8Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi falmaran, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Za a yi mata saƙar gwaninta. 9A kuma ɗauki duwatsu biyu masu daraja, a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kai. 10Sunaye shida a kowane dutse bi da bi bisa ga haihuwarsu. 11Za a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a bisa duwatsun nan kamar yadda mai yin aiki da lu'ulu'u yakan zana hatimai. Za a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya. 12A sa duwatsun a kafaɗun falmaran domin a riƙa tunawa da 'ya'yan Isra'ila. Haruna zai rataya sunayensu a kafaɗunsa a gaban Ubangiji domin a tuna da su. 13Za ku yi tsaiko biyu na zinariya, 14ku kuma yi tukakkun sarƙoki biyu na zinariya tsantsa. Za ku ɗaura wa tsaikunan nan tukakkun sarƙoƙi.
15“Ku kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji domin neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa falmaran ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. 16Ƙyallen maƙalawa a ƙirji zai zama murabba'i, a ninke shi biyu tsawonsa da fāɗinsa su zama kamu ɗaya ɗaya. 17Sai a yi jeri huɗu na duwatsun a kanta. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu. 18A jeri na biyu, a sa turkos, da saffir, da daimon. 19A jeri na uku, a sa yakinta, da idon mage, da ametis. 20A jeri na huɗu, a sa beril, da onis, da yasfa. Za a sa su cikin tsaiko na zinariya. 21A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zana sunayen kamar hatimi. 22Ku kuma yi wa ƙyallen maƙalawa a ƙirji tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa. 23Za ku yi ƙawanya biyu na zinariya, ku sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 24Ku sa tukakkun sarkoƙin nan biyu na zinariya a cikin ƙawanya biyu na zinariya da suke a gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a haɗa su daga gaba a kafaɗun falmaran. 25Za ku kuma sa sauran bakunan sarƙoƙin nan biyu a cikin tsaikuna, sa'an nan a sa shi a gaban kafaɗun falmaran. 26Ku kuma yi waɗansu ƙawane na zinariya, a sa su a sauran kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a gefe na cikin da yake manne da falmaran. 27Ku kuma yi waɗansu ƙawanya biyu na zinariya, a sa su a ƙashiyar kafaɗu biyu na falmaran daga gaba, a sama da abin ɗamaran nan. 28Za su ɗaure ƙyallen maƙalawa a ƙirji a ƙawanensa haɗe da ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya zauna bisa abin ɗamarar falmaran, don kuma kada ya yi sako-sako a bisa falmaran. 29Duk sa'ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai ɗauki sunayen 'ya'yan Isra'ila a gaban Ubangiji kullum, a kan ƙyallen maƙalawa domin nemar musu nufin Allah. 30#L.Ƙid 27.21; M.Sh 33.8; Ezra 2.63; Neh 7.65 Za ku kuma sa Urim da Tummin a kan ƙyallen maƙalawar domin su kasance a zuciyar Haruna sa'ad da ya shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai kokekoken Isra'ilawa a gaban Ubangiji.
31“Sai ku yi taguwar falmaran da shuɗi duka. 32Za a yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A yi wa wuyan shafi, sa'an nan a yi wa wuyan basitsa, wato cin wuya, domin kada ya kece. 33Za a yi wa karbun taguwar ado da fasalin 'ya'yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu. 34Za a jera su bi da bi, wato 'ya'yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya. 35Sai Haruna ya sa taguwar sa'ad da yake aiki. Za a ji ƙarar ƙararrawar a lokacin da yake shiga da lokacin da yake fita Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji don kada ya mutu.
36“Sai kuma a yi allo na zinariya tsantsa, a zana rubutu irin na hatimi a kansa haka, ‘MAI TSARKI GA UBANGIJI.’ 37Sai a ɗaura shi da shuɗiyar igiya a rawanin daga gaba. 38Haruna kuwa zai sa shi bisa goshinsa, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra'ilawa sun yi cikin miƙa sadakokinsu masu tsarki. Kullum Haruna zai riƙa sa shi bisa goshinsa don su zama karɓaɓɓu ga Ubangiji.
39“Ku saƙa zilaika da lallausan zaren lilin. Ku yi rawani da lallausan zaren lilin, ku kuma saƙa abin ɗamara mai ado.
40“Za a yi wa 'ya'yan Haruna, maza, zilaiku, da abubuwan ɗamara, da huluna don daraja da kwarjini. 41Ka sa wa Haruna, ɗan'uwanka, da 'ya'yansa maza, sa'an nan ka zuba musu mai, ka keɓe su, ka tsarkake su domin su zama firistoci masu yi mini aiki. 42Sai kuma ku yi musu mukurai na lilin don su rufe tsiraicinsu daga kwankwaso zuwa cinya. 43Haruna da 'ya'yansa maza za su sa su sa'ad da suke shiga alfarwa ta sujada ko kuwa sa'ad da suka kusaci bagade domin su yi aiki cikin Wuri Mai Tsarki domin kada su yi laifin da zai zama sanadin mutuwarsu. Wannan zai zama doka ga Haruna da zuriyarsa har abada.”
Đang chọn:
Fit 28: HAU
Tô màu
Sao chép
So sánh
Chia sẻ
Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập
@Bible Society of Nigeria 1979