Fit 2
2
Haihuwar Musa
1Sai wani mutum, Balawe, ya auro 'yar Lawi. 2#A.M 7.20; Ibr 11.23 Matar kuwa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Sa'ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har wata uku. 3Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu. 4Ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.
5Gimbiya, wato 'yar Fir'auna, ta gangaro domin ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi. 6Sa'ad da ta tuɗe kwandon ta ga jariri yana kuka. Sai ta ji tausayinsa, ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin 'ya'yan Ibraniyawa ne.”
7'Yar'uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, “In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?”
8Sai Gimbiya ta ce mata, “Je ki.” Yarinyar kuwa ta tafi ta kirawo mahaifiyar jaririn. 9Da ta zo, sai Gimbiya ta ce mata, “Dauki wannan jariri, ki yi mini renonsa, zan biya ki ladanki.” Matar kuwa ta ɗauki jaririn ta yi renonsa. 10#A.M 7.21Da jaririn ya yi girma sai ta kai shi wurin Gimbiyar. Yaro kuwa ya zama tallafinta. Ta raɗa masa suna Musa, gama ta ce, “Domin na tsamo shi daga cikin ruwa.”
Musa Ya Gudu zuwa Madayana
11 #
A.M 7.23-28
#
Ibr 11.24
Ana nan wata rana, sa'ad da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa, sai ya ga yadda suke shan wahala. Ya kuma ga wani Bamasare yana dūkan Ba'ibrane, ɗaya daga cikin 'yan'uwansa. 12Da ya waiwaya, bai ga kowa ba, sai ya kashe Bamasaren, ya turbuɗe shi cikin yashi. 13Kashegari da ya sāke fita, sai ya ga waɗansu Ibraniyawa biyu suna faɗa da juna. Ya ce wa wanda yake ƙwaran ɗan'uwansa, “Me ya sa kake bugun ɗan'uwanka?”
14Ya amsa, ya ce, “Wa ya naɗa ka sarki ko alƙali a bisanmu? So kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren?”
Sai Musa ya tsorata, ya ce, “Assha, ashe, an san al'amarin!” 15#A.M 7.29; Ibr 11.27 Da Fir'auna ya ji, sai ya nema ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu daga gaban Fir'auna, ya tafi, ya zauna a ƙasar Madayana. Da ya kai, sai ya zauna a bakin wata rijiya.
16Ana nan waɗansu 'yan mata bakwai, 'ya'yan firist na Madayana suka zo su cika komaye da ruwa domin su shayar da garken mahaifinsu. 17Sai makiyaya suka zo, suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su, ya kuma shayar da garkensu. 18Lokacin da suka koma wurin mahaifinsu, Reyuwel, wato Yetro, ya ce musu, “Yaya aka yi yau, kuka komo da sauri haka?”
19Sai suka ce, “Wani Bamasare ne ya cece mu daga hannun makiyaya, har ya ɗebo ruwa, ya shayar da garkenmu.”
20Reyuwel kuwa ya ce wa 'ya'yansa mata, “A ina yake? Me ya sa ba ku zo da shi ba? Ku kirawo shi, ya zo, ya ci abinci.”
21Musa kuwa ya yarda ya zauna tare da Reyuwel. Sai ya aurar wa Musa da 'yarsa Ziffora. 22Ita kuwa ta haifa masa ɗa, ya raɗa masa suna Gershom, gama ya ce, “Baƙo ne ni, a baƙuwar ƙasa.”
23Ana nan, a kwana a tashi, sai Sarkin Masar ya rasu. Jama'ar Isra'ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun Allah. 24#Far 15.13,14 Allah kuwa ya ji nishinsu, sai ya tuna da alkawarinsa da ya yi wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. 25Allah ya dubi jama'ar Isra'ila, ya kuwa kula da su.
Đang chọn:
Fit 2: HAU
Tô màu
Sao chép
So sánh
Chia sẻ
Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập
@Bible Society of Nigeria 1979