Biểu trưng YouVersion
Biểu tượng Tìm kiếm

Fit 11

11
Musa Ya Hurta Mutuwar 'Ya'yan Fari
1Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yanzu dai zan ƙara bugun Fir'auna da Masarawa sau ɗayan nan kawai da annoba. Bayan wannan zai sake ku. Sa'ad da ya bar ku ku tafi, zai iza ƙyeyarku. 2Sai ka faɗa wa jama'a, kowane mutum da kowace mace su roƙi kayan ado na azurfa da na zinariya daga wurin maƙwabtansu.” 3Ubangiji kuwa ya sa jama'a su yi farin jini a idanun Masarawa. Musa kuwa ya zama babban mutum a ƙasar Masar a gaban fādawan Fir'auna da kuma gaban jama'ar.
4Musa ya ce wa Fir'auna, “Ga abin da Ubangiji ya faɗa, ‘A wajen tsakar dare zan ratsa cikin Masar. 5Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir'auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu. 6Za a kuwa yi kuka mai zafi ko'ina a ƙasar Masar irin wanda ba a taɓa yi ba, ba kuma za a ƙara yi ba. 7Amma ko kare ba zai yi wa wani mutum ko dabba na Isra'ila haushi ba, domin ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masarawa da Isra'ilawa.’ 8Sa'an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama'arka!’ Sa'an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna a husace.
9Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir'auna ba zai kasa kunne gare ka ba, sai na ƙara aikata waɗansu mu'ujizai cikin ƙasar Masar.” 10Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu'ujizai a gaban Fir'auna. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, bai kuwa saki Isra'ilawa daga ƙasarsa ba.

Đang chọn:

Fit 11: HAU

Tô màu

Sao chép

So sánh

Chia sẻ

None

Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập