Biểu trưng YouVersion
Biểu tượng Tìm kiếm

Mattiyu Gabatarwa

Gabatarwa
Gabatarwa
Mattiyu a bishararsa ya gabatar da Yesu a matsayin Kiristi wanda ya cika Nassosin Yahudawa. Waɗansu masana sun kira Bisharar Mattiyu “mafi Yahudanci” na Bisharu. An gabatar da koyarwar Yesu a jawabai guda biyar. Hanyar da za a shirya koyarwar Yesu sun sa masu karatu na Yahudawa suka tuna da Musa, domin al’adunsu sun koyar cewa Musa ya rubuta littattafai biyar na Doka (Attaura). Wannan kamanni ya ba da ra’ayin cewa marubucin Mattiyu yana gabatar da Yesu a matsayin “sabon Musa.” Littafin kuma ya ci gaba da ambata Nassosin Yahudawa, yana amfani da salon rubutun Yahudawa, yana kuma ɗaukan alamun da Yahudawa suka saba da su a lokacin. Masana kuma suna kira Mattiyu “Bisharar ikkilisiya”, saboda littafin ya mai da hankali a kan Yesu a matsayin Ubangiji wanda ya tashi daga matattu, a kan mulkin sama, da kuma a kan ikkilisiya kanta. Tabbatacce, Mattiyu ne Bishara kaɗai da ta yi amfani da kalmar Girik ta “ikkilisiya.” Sau da dama Mattiyu yakan nuna Yesu tsaye “waje da lokaci,” yana gabatar da ayyukan Yesu a yanayi da kuma cikin tarihi da kuma ɗaukakarsa a matsayin madawwami, Ubangiji da ya tashi daga matattu.

Tô màu

Chia sẻ

Sao chép

None

Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập

YouVersion sử dụng cookies để cá nhân hóa trải nghiệm của bạn. Bằng cách sử dụng trang web của chúng tôi, bạn chấp nhận việc chúng tôi sử dụng cookies như được mô tả trong Chính sách Bảo mậtcủa chúng tôi