1
Fit 13:21-22
Littafi Mai Tsarki
HAU
Da rana Ubangiji yakan yi musu jagora da al'amudin girgije, da dare kuwa da al'amudin wuta, domin ya ba su haske domin su iya tafiya dare da rana. Al'amudan nan biyu kuwa, na girgijen da na wutar, ba su daina yi wa jama'a jagora ba.
So sánh
Khám phá Fit 13:21-22
2
Fit 13:17
Da Fir'auna ya bar jama'a su tafi, Allah bai bi da su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ta fi kusa, gama Allah ya ce, “Don kada jama'a su sāke tunaninsu sa'ad da suka ga yaƙi, su koma Masar.”
Khám phá Fit 13:17
3
Fit 13:18
Amma Allah ya kewaya da jama'a ta hanyar jeji, wajen Bahar Maliya. Isra'ilawa kuwa suka fita daga ƙasar Masar da shirin yaƙi.
Khám phá Fit 13:18