W.W 2
2
1Ni fure ce na Sharon,
Furen bi-rana na cikin kwari.
2Kamar yadda furen bi-rana yake a cikin ƙayayuwa,
Haka ƙaunatacciyata take a cikin sauran mata.
3Kamar yadda itacen gawasa yake a cikin itatuwan jeji,
Haka ƙaunataccena yake a cikin sauran maza.
Da farin ciki na zauna a inuwarsa,
Ina jin daɗin halinsa ƙwarai.
4Ya kai ni babban ɗakin da ake liyafa,
Ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.
5Ka ciyar da ni da wainar zabibi,
Ka ba ni 'ya'yan gawasa in sha in wartsake!
Gama na cika da sha'awarka.
6Bari ka ta da kaina da hannun hagunka,
Ka rungume ni da hannun damanka.
7Ku 'yan matan Urushalima,
Ku rantse da bareyi, da batsiyoyi,
Ba za ku shiga tsakaninmu ba,
Ku bar ta kurum.
Waƙa ta Biyu
8Na ji muryar ƙaunataccena!
Ya zo a guje daga kan tuddai,
Ya sheƙo daga tuddai zuwa wurina.
9Ƙaunataccena kamar barewa yake,
Kamar sagarin kishimi.
Ga shi can, yana tsaye a bayan katangarmu.
Yana leƙe ta tagogi,
Yana kallona ta cikin asabari.
10Ƙaunataccena ya yi magana da ni.
Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa.
11Gama lokacin sanyi ya wuce,
Ruwa kuma ya ɗauke.
12Furanni suna hudowa a itatuwa ko'ina.
Lokacin raira Waƙoƙi ya yi,
Lokacin da kurciyoyi suke kuka ya yi.
13'Ya'yan ɓaure sun nuna,
Tohon inabi yana ƙanshi.
Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa!
14Ya kurciyata kina zaune a kogon dutse mai tsayi.
Bari in ga fuskarki, in kuma ji muryarki,
Gama muryarki tana da daɗin ji,
Fuskarki kuma tana da kyan gani.
15Ku kama mana 'yan ƙananan diloli
Waɗanda suke ɓata gonakin inabi,
Gama gonakin inabinmu sun yi fure.
16Ƙaunataccena nawa ne, ni ma tasa ce,
Yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana,
17Har hurowar iskar safiya,
Sa'ad da duhu ya kawu.
Komo ya ƙaunataccena, yi kamar barewa,
Kamar sagarin kishimi a kan duwatsu.
Currently Selected:
W.W 2: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979