YouVersion Logo
Search Icon

W.W 1

1
Amarya da 'Yan Matan Urushalima
1 # 1Sar 4.32 Ga waƙar Sulemanu mafi daɗi.
Waƙa ta Fari
2Leɓunanka sun lulluɓe ni da sumba,
Ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
3Akwai ƙanshi kuma kewaye da kai,
Jin amon sunanka yana tunasar da ni.
Ba wata matar da za ta ƙi ƙaunarka.
4Ka ɗauke ni mana, mu gudu,
Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka.
Da yake kana nan za mu yi farin ciki,
Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki.
Ya dace a ƙaunace ka!
5Rana ta sa na zama akawala kyakkyawa.
Matan Urushalima, bisa ga launi, ni ƙasa ƙasa ce,
Kamar alfarwar hamada,
Kamar labulen fādar Sulemanu.
6Kada ka raina ni saboda launina,
Domin rana ta dafe ni.
'Yan'uwana suna fushi da ni,
Sun sa ni aiki a gonar inabi.
Ba ni da zarafin da zan lura da kaina.
7Faɗa mini, ƙaunataccena,
Ina za ka kai garkenka kiwo?
Ina za su huta sa'ad da rana ta take?
Ina zan neme ka a cikin garkunan makiyaya?
8Mafi kyau cikin mata, ashe, ba ki san wurin ba?
Tafi, ki bi garken,
Ki samar wa awakinki wurin kiwo
Kusa da alfarwan makiyaya.
Amarya da Ango
9Ke ƙaunatacciyata, kina ɗauke hankalina
Kamar yadda goɗiya take ɗauke hankalin ingarmun karusan Fir'auna.
10Kitsonki yana da kyau a kumatunki,
Ya sauka a wuyanki kamar lu'ulu'ai.
11Mu kuma za mu ƙera miki sarƙar zinariya,
A yi miki ado da azurfa.
12A sa'ad da sarki yake kan kujerarsa,
Yana jin daɗin ƙanshin turarena ƙwarai.
13Ƙaunataccena yana da ƙanshin mur
Lokacin da yake kwance a ƙirjina.
14Ƙaunataccena kamar furen jeji yake
Wanda yake huda a gonar inabi a En-gedi.
15Ke kyakkyawa ce ƙwarai, kyakkyawa ce ke, ya ƙaunatacciyata,
Idonki suna haskaka da ƙauna.
16Kai kyakkyawa ne ƙwarai, ya ƙaunataccena, kana da bansha'awa.
Koriyar ciyawa ita ce gadonmu.
17Itatuwan al'ul su ne jigajigan gidanmu,
Itatuwan fir su ne rufin gidan.

Currently Selected:

W.W 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in