YouVersion Logo
Search Icon

Rut 3

3
Bo'aza da Rut a Masussuka
1Wata rana, Na'omi ta ce wa Rut, “'Yata, ya kamata in nemar miki miji don ki sami gida inda za ki huta, ki ji daɗi. 2Bo'aza wanda kika yi aiki da barorinsa danginmu ne. Ga shi, zai tafi sussukar sha'ir a masussuka da maraice. 3Sai ki yi wanka, ki shafa man ƙanshi, ki yafa tufafinki na ado, ki tafi masussukar, amma kada ki bari ya san zuwanki, sai bayan da ya riga ya ci ya sha. 4Sa'ad da ya kwanta, sai ki lura da inda ya kwanta, sa'an nan ki tafi, ki buɗe mayafinsa a wajen ƙafafunsa, ki kwanta a ciki. Zai kuwa faɗa miki abin da za ki yi.”
5Rut ta amsa, “Zan yi dukan abin da kika faɗa.”
6Rut kuwa ta gangara zuwa masussukar, ta yi yadda surukarta ta faɗa mata. 7Sa'ad da Bo'aza ya ci ya sha yana cikin jin daɗi, sai ya je ya kwanta kusa da tsibin tsabar sha'ir. Sa'an nan Rut ta tafi a hankali, ta buɗe mayafin da ya rufa da shi wajen ƙafafunsa, ta kwanta a ciki. 8Da tsakar dare, sai mutumin ya farka a firgice, ya juya, sai ga mace kwance a wajen ƙafafunsa. 9Ya ce, “Wace ce?”
Sai ta amsa, “Ni ce Rut, baranyarka, sai ka rufe ni da mayafinka, gama kai dangi ne na kusa.”
10Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya sa miki albarka 'yata, yanzu kin nuna alheri mafi girma fiye da na dā da yake ba ki nemi saurayi, matalauci ko attajiri ba. 11Yanzu dai, 'yata, kada ki damu, zan yi miki dukan abin da kika roƙa, gama dukan mutanen garin sun sani ke macen kirki ce. 12#Rut 2.20 Gaskiya ce, ni dangi na kusa ne, amma akwai wanda yake dangi na kusa fiye da ni. 13Ki dakata nan sai gobe, da safe za mu gani, idan shi zai cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Idan ya cika, to, da kyau, amma idan bai cika ba, na rantse da Allah mai rai, zan cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Ki kwanta sai da safe.” 14Sai ta kwanta a wajen ƙafafunsa har safiya. Sa'an nan ta tashi tun da jijjifi kafin a iya gane fuskar mutum, gama ba ya so a sani mace ta zo masussukar.
15Bo'aza ya ce mata, “Kawo mayafinki, ki shimfiɗa shi.” Sai ta shimfiɗa mayafin, ya zuba mata sha'ir ya kusa garwa huɗu ya aza mata a kā. Sa'an nan ta koma gari.
16Lokacin da ta zo wurin surukarta, sai surukarta ta ce mata, “'Yata, ina labari?”
Sai ta faɗa mata dukan abin da mutumin ya faɗa mata. 17Ta kuma ce, “Ga sha'ir da ya ba ni, gama ya ce, ‘Ba za ki koma wurin surukarki hannu wofi ba.’ ” 18Sai surukarta ta ce, “Ki jira dai, 'yata, har ki ga yadda al'amarin zai zama, gama mutumin ba zai huta ba, sai ya daidaita al'amarin a yau.”

Currently Selected:

Rut 3: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in