Rut 2
2
Rut a Gonar Bo'aza
1Na'omi tana da wani dangin mijinta, Elimelek, sunansa Bo'aza, shi kuwa attajiri ne. 2#L.Fir 19.9,10; M.Sh 24.19 Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na'omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.”
Na'omi ta ce mata, “Ki tafi, 'yata.” 3Rut ta tafi wata gona, tana bin bayan masu girbi, tana kala. Ta yi sa'a kuwa ta fāɗa a gonar Bo'aza, dangin Elimelek.
4Sai ga Bo'aza ya zo daga Baitalami, ya ce wa masu girbi, “Salamu alaikun.”
Suka amsa, “Alaika salamu.”
5Sa'an nan Bo'aza ya tambayi baransa da yake shugaban masu girbin, ya ce, “'Yar wace ce wannan?”
6Baran ya ce, “Ita 'yar Mowab ce wadda ta zo tare da Na'omi daga ƙasar Mowab. 7Ita ce ta ce mana, ‘In kun yarda, ku bar ni in bi bayan masu girbin, ina kala.’ Haka ta yi ta kala tun da sassafe har yanzu ba hutu, sai dai 'yar shaƙatawar da ta yi kaɗan.”
8Sa'an nan sai Bo'aza ya ce wa Rut, “Kin ji, 'yata, kada ki bar wannan gona ki tafi wata gona domin kala, amma ki riƙa bin 'yan matan gidana. 9Ki kula da gonar da suke girbi, ki bi su. Ga shi, na riga na umarci barorina kada su dame ki. Sa'ad da kika ji ƙishirwa, sai ki tafi ki sha ruwa a tuluna, wanda barorin suka ɗebo.”
10Sai Rut ta rusuna har ƙasa, ta ce masa, “Me ya sa na sami tagomashi a gare ka, har da za ka kula da ni, ni da nake baƙuwa?”
11Amma Bo'aza ya ce mata, “An faɗa mini dukan abin da kika yi wa surukarki tun lokacin da mijinki ya rasu, da yadda kika bar iyayenki da ƙasarku, kika zo wurin mutanen da ba ki taɓa saninsu ba a dā. 12Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda kika zo neman mafaka gare shi, ya sāka miki da cikakken lada saboda abin da kika yi.”
13Rut ta ce, “Shugaba, kā yi mini alheri ƙwarai, gama kā ta'azantar da ni, kā yi wa baiwarka maganar alheri, ko da yake ni ba ɗaya daga cikin barorinka ba ce.”
14Da lokacin cin abinci ya yi, sai Bo'aza ya kira Rut, ya ce, “Zo nan ki ci abinci, ki riƙa tsoma lomarki a ruwan inabin da aka surka.” Sai ta zo, ta zauna kusa da masu girbin. Shi kuwa ya ba ta tumun hatsi. Ta ci, ta ƙoshi har ta bar saura. 15Sa'ad da ta tashi, za ta yi kala, sai Bo'aza ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku bar ta, ta yi kala a tsakanin tarin dammunan, kada ku hana ta. 16Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.” 17Ta yi ta kala a gonar har yamma. Ta sussuka abin da ta kalata, ta sami tsaba wajen garwa biyu. 18Ta ɗauka, ta koma gari, ta nuna wa surukarta abin da ta kalato. Ta kuma kawo mata sauran abincin da ta ci ta ƙoshi har ta rage.
19Surukarta kuma ta ce mata, “A ina kika yi kala yau? A gonar wa kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga wannan mutum wanda ya kula da ke.”
Sai ta faɗa mata sunan mutumin da ta yi kala a gonarsa, ta ce, “Sunan mutumin da na yi kala a gonarsa yau, Bo'aza.”
20 #
L.Fir 25.25
Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.”
21Rut kuma, mutuniyar Mowab, ta ce, “Banda wannan ma, ya ce mini, ‘Ki riƙa bin barorina, har lokacin da suka gama mini girbin.’ ”
22Sa'an nan Na'omi ta ce wa Rut, “Madalla, 'yata, ki riƙa bin 'yan matan gidansa, kada ki tafi wata gona dabam.” 23Sai ta riƙa bin 'yan matan gidan Bo'aza. Ta yi ta kala har aka gama girbin sha'ir da na alkama, tana zaune tare da surukarta, wato Na'omi.
Currently Selected:
Rut 2: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979