YouVersion Logo
Search Icon

W.Yah 15

15
Mala'iku Masu Bala'i Bakwai
1Na kuma ga wata alama a Sama, mai girma, mai banmamaki, mala'iku bakwai masu bala'i bakwai, waɗanda suke bala'in ƙarshe, don su ne iyakacin fushin Allah.
2Sai na ga wani abu kamar bahar na gilas, gauraye da wuta, na kuma ga waɗanda suka yi nasara da dabbar nan, da siffarta, da kuma lambar sunanta, a tsaitsaye a bakin bahar na gilas, da molayen yabon Allah a hannunsu. 3#Fit 15.1 Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa,
“Ayyukanka manya ne, masu banmamaki,
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki!
Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma,
Ya Sarkin al'ummai.
4 # Irm 10.7; Zab 86.9 Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji,
Ya kuma ɗaukaka sunanka?
Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki.
Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada,
Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”
5 # Fit 38.21 Bayan wannan na duba, ga Wuri Mafi Tsarki a buɗe a Haikali a Sama. 6Sai mala'ika bakwai ɗin nan masu bala'i bakwai suka fito daga Haikalin, saye da tufafin lilin mai tsabta, mai ɗaukar iko, da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu. 7Sai ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan guda huɗu, ta ba mala'ikun nan bakwai tasoshi bakwai na zinariya, a cike da fushin Allah, shi da yake a raye har abada abadin. 8#Fit 40.34; 1Sar 8.10,11; 2Tar 5.13,14; Ish 6.4 Sai Haikalin ya cika da hayaƙi mai fitowa daga ɗaukakar Allah da ikonsa. Ba mai iya shiga Haikalin nan, sai bayan bala'i bakwai na mala'ikun nan bakwai sun ƙare.

Currently Selected:

W.Yah 15: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in