W.Yah 14
14
Waƙar 144,000 Ɗin
1 #
Eze 9.4; W.Yah 7.3 Sa'an nan na duba, sai ga Ɗan Ragon nan a tsaye a kan Dutsen Sihiyona, akwai kuma mutum dubu ɗari da dubu arba'in da huɗu tare da shi, waɗanda aka rubuta sunansa, da sunan Ubansa, a goshinsu. 2Sai na ji wata murya daga Sama kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, muryar da na ji kuwa, kamar ta masu molo ce na kiɗan molo. 3Suna raira wata sabuwar waƙa a gaban kursiyin, a gaban rayayyun halittan nan huɗu, da kuma a gaban dattawan nan. Ba mai iya koyon waƙar nan, sai mutum dubu ɗari da dubu arba'in da huɗu ɗin nan, waɗanda aka fanso daga duniya. 4Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma, 5#Zaf 3.13 ba wata ƙarya a bakinsu, domin su marasa aibu ne.
Sanarwar Mala'iku Uku Ɗin
6Sa'an nan na ga wani mala'ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da jama'a. 7Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, domin lokacinsa na yin hukunci ya yi. Ku yi masa sujada, shi da ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma maɓuɓɓugan ruwa.”
8 #
Ish 21.9; Irm 51.8; W.Yah 18.2 Sai kuma mala'ika na biyu ya biyo, yana cewa, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ita da ta zuga dukkan al'ummai su yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita.”
9Sai kuma mala'ika na uku ya biyo, yana ɗaga murya da ƙarfi, yana cewa, “Duk mai yi wa dabbar nan da siffarta sujada, wanda kuma ya yarda a yi masa alama a goshinsa, ko a hannunsa, 10#Ish 51.17; Far 19.24; Eze 38.22 zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa, za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala'iku tsarkaka, da kuma Ɗan Ragon. 11#Ish 34.10 Hayaƙin azabar nan tasu ya dinga tashi har abada abadin, ba su da wani rangwame dare da rana, wato, waɗannan masu yi wa dabbar nan da siffarta sujada, da kuma duk wanda ya yarda aka yi masa alamar sunanta.”
12Wannan yana nuna jimirin tsarkaka, masu kiyaye umarnin Allah da kuma bangaskiya ga Yesu.
13Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”
Girbe Duniya
14 #
Dan 7.13
Sa'an nan na duba, sai ga wani farin gajimare, da wani kamar Ɗan Mutum a zaune a kan gajimaren, da kambin zinariya a kansa, da kakkaifan lauje a hannunsa. 15#Yow 3.13 Sai mala'ika ya fito daga Haikalin, yana magana da murya mai ƙarfi da wanda yake a zaune a kan gajimaren, yana cewa, “Ka sa laujenka ka yanke, don lokacin yanka ya yi, amfanin duniya ya nuna sarai.” 16Sai wanda yake a zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa zuwa duniya, aka girbe amfanin duniya.
17Wani mala'ika kuma ya fito daga Haikali a Sama, shi ma kuwa yana da kakkaifan lauje. 18Sai kuma wani mala'ika ya fito daga bagadin ƙona turare, wato, mala'ikan da yake da iko da wutar, ya yi magana da murya mai ƙarfi da wannan mai kakkaifan lauje, ya ce, “Ka sa laujenka ka yanke nonnan inabin zuwa duniya, don inabin ya nuna.” 19Sai mala'ikan ya wurga laujensa duniya, ya tattara inabin duniya, ya zuba a cikin babbar mamatsar inabi ta fushin Allah. 20#Ish 63.3; Mak 1.15; W.Yah 19.15 Aka tattake mamatsar inabin a bayan gari, jini kuma ya yi ta gudana daga mamatsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil metan.
Currently Selected:
W.Yah 14: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979