Bible App logo
Search Icon

Zab 74

74
Addu'ar Neman Ceton Al'ummar Allah
1Don me ka yashe mu haka, ya Allah?
Za ka yi ta fushi da jama'arka har abada ne?
2Ka tuna da jama'arka waɗanda ka zaɓa su zama naka tuntuni,
Ka tuna da jama'arka waɗanda ka fansa,
Don su zama kabilarka.
Ka tuna da Dutsen Sihiyona, inda zatinka yake!
3Ka zo, ka yi yawo a wannan kufai,
Abokan gābanmu sun lalatar da kome na cikin Haikali!
4Abokan gābanka suka yi sowa ta nasara
A inda akan sadu da kai,
Sun ƙwace Haikalin.
5Suna kama da masu saran itace,
Suna saran itatuwa da gaturansu.
6Da gaturansu da gudumarsu,
Sun ragargaje ƙyamaren da aka yi da katako.
7Sun sa wa Haikalinka wuta,
Sun ƙazantar da wurin da akan yi maka sujada,
Sun farfashe shi duk.
8Sun yi niyya su murƙushe mu sarai,
Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.
9Ba sauran tsarkakan alamu,
Ba sauran annabawan da suka ragu,
Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.
10Ya Allah, har yaushe abokan gābanmu za su yi ta yi mana ba'a?
Za su yi ta zargin sunanka har abada ne?
11Me ya sa ka ƙi taimakonmu?
Ka tasar musu ka hallaka su!
12Amma ya Allah, kai ne Sarkinmu tun daga farko,
Ka yi nasara da duniya.
13 # Fit 14.21 Da ƙarfin ikonka ka raba teku,
Ka farfashe kawunan dodannin ruwa,
14 # Ayu 41.1; Zab 104.26; Ish 27.1 Ka ragargaje kawunan kadduna,
Ka kuwa ba mutanen hamada su ci.
15Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu,
Ka sa manyan koguna su ƙafe.
16Ka halicci yini da dare,
Ka sa rana da wata a wurarensu.
17Ka yi wa duniya kan iyaka,
Ka kuwa yi lokatan damuna da na rani.
18Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a,
Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.
19Kada ka ba da jama'arka marasa taimako
A hannun mugayen maƙiyansu,
Kada ka manta da jama'arka waɗanda ake tsananta musu!
20Ka tuna da alkawarin da ka yi mana,
Akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar!
21Kada ka bari a kori waɗanda ake zalunta,
Amma bari matalauta da masu mayata su yabe ka.
22Ka tashi, ya Allah, ka kāre kanka!
Ka tuna fa, marasa tsoronka suna ta yi maka ba'a dukan yini!
23Kada ka manta da hargowar maƙiyanka,
Kada ka manta da hayaniyar da magabtanka suke ta yi.

Currently Selected:

Zab 74: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for Zab 74