Zab 62
62
Allah ne kaɗai Mafaka
1Ga Allah kaɗai na dogara,
Cetona daga gare shi yake fitowa.
2Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,
Shi ne kariyata,
Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.
3Har yaushe dukanku za ku fāɗa wa wani don ku yi nasara da shi,
Kamar rusasshen garu,
Ko kuma dangar da ta fāɗi?
4Ba abin da kuke so, sai ku ƙasƙantar da shi daga maƙaminsa na daraja,
Kuna jin daɗin yin ƙarairayi.
Kuna sa masa albarka,
Amma a zuciyarku la'antarwa kuke yi.
5Ga Allah kaɗai na dogara,
A gare shi na sa zuciyata.
6Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,
Shi ne kariyata,
Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.
7Cetona da darajata daga Allah ne,
Shi ne ƙaƙƙarfan makiyayina,
Shi ne mafakata.
8Ya jama'ata, ku dogara ya Allah a kowane lokaci!
Ku faɗa masa dukan wahalarku,
Gama shi ne mafakarmu.
9Talakawa kamar shaƙar numfashi suke,
Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani.
Ko an auna su a ma'auni, sam ba su da nauyin kome,
Sun fi numfashi shakaf.
10Kada ku dogara da aikin kama-karya.
Kada ku sa zuciya za ku ci ribar kome ta wurin fashi.
In kuwa dukiyarku ta ƙaru,
Kada ku dogara gare ta.
11Sau ɗaya Allah ya faɗa,
Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.
12 #
Ayu 34.11; Irm 17.10; Mat 16.27; Rom 2.6; W.Yah 2.23 Madawwamiyar ƙauna, ta Ubangiji ce.
Kai kanka, ya Ubangiji, kake sāka wa
Kowane mutum bisa ga ayyukansa.
Currently Selected:
Zab 62: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979