Zab 46
46
Allah ne Mafakarmu da Ƙarfinmu
1Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.
2Saboda haka ba za mu ji tsoro ba,
Ko da duniya za ta girgiza,
Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,
3Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa,
Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun.
4Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah,
Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.
5Allah yana zaune cikin birnin,
Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau.
Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.
6An kaɓantar da sauran al'umma, mulkoki suka girgiza,
Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke.
7Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu,
Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!
8Zo ku ga abin da Ubangiji ya yi!
Dubi irin ayyukan al'ajabi da ya yi a duniya!
9Ya hana yaƙoƙi ko'ina a duniya,
Yana karya bakkuna, yana lalatar da māsu,
Yana ƙone karusai da wuta.
10Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah,
Maɗaukaki ne cikin sauran al'umma,
Maɗaukaki kuma a duniya!”
11Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu,
Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!
Currently Selected:
Zab 46: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979