1
Zab 46:10
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah, Maɗaukaki ne cikin sauran al'umma, Maɗaukaki kuma a duniya!”
Compare
Explore Zab 46:10
2
Zab 46:1-2
Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, Ko da duniya za ta girgiza, Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku
Explore Zab 46:1-2
3
Zab 46:4-5
Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah, Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki. Allah yana zaune cikin birnin, Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau. Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.
Explore Zab 46:4-5
4
Zab 46:9
Ya hana yaƙoƙi ko'ina a duniya, Yana karya bakkuna, yana lalatar da māsu, Yana ƙone karusai da wuta.
Explore Zab 46:9