Zab 44
44
Addu'ar Neman Ceto
1Da kunnuwanmu muka ji, ya Allah,
Kakanninmu suka faɗa mana,
Manya manyan abubuwa da ka aikata a lokacinsu,
A zamanin dā,
2Yadda kai da kanka ka kori arna,
Ka dasa jama'arka a ƙasarsu,
Yadda ka hori sauran al'umma,
Amma ka sa jama'arka su wadata.
3Ba da takubansu suka ci ƙasar ba,
Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba,
Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka,
Ta wurin tabbatar musu kana tare da su,
Kana nuna musu kana ƙaunarsu.
4“Ya Allah, kai ne Sarkina,
Ka ba jama'arka nasara.
5Da ikonka muka kori abokan gābanmu,
Saboda kasancewarka tare da mu
Muka rinjayi magabtanmu.
6Ban dogara ga bakana ba,
Takobina kuwa ba zai cece ni ba.
7Amma ka cece mu daga abokan gābanmu,
Ka kori waɗanda suke ƙinmu.
8Za mu yabe ka kullum,
Mu yi maka godiya har abada.”
9Amma yanzu, ya Allah, ka yashe mu,
Ka bari aka kore mu,
Ba ka ƙara fita ka yi tafiya tare da sojojinmu ba.
10Ka sa muka gudu daga gaban abokan gābanmu,
Suka ƙwace abin da muke da shi.
11Ka bari aka yanyanka mu kamar tumaki,
Ka warwatsar da mu a baƙuwar ƙasa.
12Ka sayar da jama'arka
A bakin 'yan kuɗi ƙalilan,
Ba ka ci ribar cinikin ba.
13Maƙwabtanmu suna yi mana dariya saboda kai,
Suna yi mana ba'a, sun maishe mu abin wasa.
14Ka maishe mu abin raini a wurin arna,
Suna kaɗa mana kai, suna raina mu.
15Kullum a cikin kunya nake,
Kunya ta lulluɓe ni ɗungum,
16Saboda dukan wulakanci,
Da zagin da nake sha daga maƙiyana da abokan gābana.
17Dukan wannan ya same mu,
Ko da yake ba mu manta da kai ba,
Ba mu kuma ta da alkawarin da ka yi da mu ba.
18Ba mu ci amanarka ba,
Ba mu ƙi yin biyayya da umarnanka ba.
19Duk da haka ka ƙi taimakonmu da namomin jejin nan,
Ka bar mu a cikin duhu baƙi ƙirin.
20Da a ce mun daina yin sujada ga Allahnmu,
Muka yi addu'a ga gumaka,
21Hakika ka gane,
Domin ka san asirin tunanin mutane.
22 #
Rom 8.36
Ya Allah, saboda kai ne ake karkashe mu a kowane lokaci,
Ake kuma maishe mu kamar tumakin da za a yanyanka.
23Ka tashi, ya Ubangiji! Me ya sa kake zama kamar mai barci?
Ka tashi! Kada ka yashe mu har abada!
24Me ya sa ka ɓuya mana?
Kada ka manta da ƙuncinmu da wahalarmu!
25Mun fāɗi, an turmushe mu a ƙasa,
An bar mu kwance cikin ƙura.
26Ka tashi ka taimake mu!
Ka fanshe mu saboda madawwamiyar ƙaunarka!
Currently Selected:
Zab 44: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979