Zab 45
45
Waƙar Ɗaurin Auren Sarki
1Kwanyata ta cika da kyawawan kalmomi,
Lokacin da nake tsara waƙar sarki,
Harshena kuwa kamar alkalami ne na ƙwararren marubuci.
2Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane,
Kai mai kyakkyawan lafazi ne,
Kullum Allah yakan sa maka albarka!
3Ka sha ɗamara da takobinka, ya Maɗaukakin Sarki,
Kai mai iko ne, Maɗaukaki!
4Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara,
Domin ka tsare gaskiya da adalci.
Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.
5Kibanka suna da tsini,
Suna huda zuciyar abokan gābanka,
Al'ummai suna fāɗuwa ƙasa a ƙafafunka.
6 #
Ibr 1.8,9 Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin!
Kana mulkin mallakarka da adalci.
7Kana ƙaunar abin da yake daidai,
Kana ƙin abin da yake mugu.
Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka,
Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.
8Tufafinka suna ƙanshin turaren mur, da na aloyes, da na kashiya,
A kowace fādar hauren giwa, mawaƙa suna yi maka waƙar.
9Daga cikin matan da suke fadarka, har da 'ya'yan sarakuna.
A daman kursiyinka kuwa ga sarauniya a tsaye.
Tana saye da kayan ado na zinariya mafi kyau duka.
10Ki ji abin da zan faɗa, ya ke amaryar sarki,
Ki manta da mutanenki da danginki.
11Saboda ke kyakkyawa ce sarki zai so ki,
Shi ne maigidanki, sai ki yi masa biyayya.
12Mutanen Taya za su kawo miki kyautai,
Attajirai za su zo su sami farin jini a gare ki.
13Gimbiya tana fāda, kyakkyawa ce ainun,
Da zaren zinariya aka saƙa rigarta,
14Aka kai ta wurin sarki tana saye da riga mai ado.
Ga 'yan matanta a biye,
Aka kawo su wurin sarki.
15Da farin ciki da murna suka zo,
Suka shiga fādar sarki.
16Za ka haifi 'ya'ya maza da yawa,
Waɗanda za su maye matsayin kakanninka,
Za ka sa su zama masu mulkin duniya duka.
17Waƙata za ta sa a yi ta tunawa da sunanka har abada,
Dukan jama'a za su yabe ka a dukan zamanai masu zuwa.
Currently Selected:
Zab 45: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979