Zab 32
32
Albarkar Gafarar Zunubi
1 #
Rom 4.7,8 Mai farin ciki ne mutumin da aka gafarta masa zunubansa,
Mai farin ciki ne kuma wanda aka gafarta masa laifofinsa.
2Mai farin ciki ne wanda Ubangiji bai zarge shi a kan wani laifi ba,
Wanda ba algus ko kaɗan a cikinsa.
3Sa'ad da ban hurta zunubaina ba,
Na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini.
4Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji,
Ƙarfina duka ya ƙare sarai,
Kamar yadda laima yake bushewa,
Saboda zafin bazara.
5Sa'an nan na hurta zunubaina gare ka,
Ban ɓoye laifofina ba.
Na ƙudurta in hurta su gare ka,
Ka kuwa gafarta dukan laifofina.
6Saboda haka dukan jama'arka masu biyayya,
Za su yi addu'a gare ka, lokacin bukata.
Sa'ad da babbar rigyawa ta malalo,
Ba za ta kai wurinsu ba.
7Kai ne maɓoyata,
Za ka cece ni daga wahala.
Ina raira waƙa da ƙarfi saboda cetonka,
Domin ka kiyaye ni.
8Ubangiji ya ce, “Zan koya maka hanyar da za ka bi,
Zan koya maka, in kuma ba ka shawara.
9Kada ka zama wawa kamar doki ko alfadari,
Wanda dole sai da linzami, da ragama za a sarrafa shi,
Sa'an nan yă yi maka biyayya.”
10Tilas ne mugu yă sha wahala,
Amma masu dogara ga Ubangiji,
Madawwamiyar ƙaunarsa tana kiyaye su.
11Dukanku adalai, ku yi murna,
Ku yi farin ciki,
Saboda abin da Ubangiji ya yi!
Dukanku da kuke yi masa biyayya,
Ku yi sowa ta farin ciki!
Currently Selected:
Zab 32: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979