Zab 33
33
Waƙar Yabo
1Dukanku adalai ku yi murna,
A kan abin da Ubangiji ya yi,
Ku yabe shi, ku da kuke masa biyayya!
2Ku kaɗa garaya, kuna yi wa Ubangiji godiya.
Ku raira masa waƙa, da kayan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya.
3Ku raira masa sabuwar waƙa,
Ku kaɗa garaya da gwaninta,
Ku kuma raira waƙa da ƙarfi!
4Kalmomin Ubangiji gaskiya ne,
Ayyukansa duka kuwa abin dogara ne.
5Ubangiji yana ƙaunar abin da yake na adalci da gaskiya,
Madawwamiyar ƙaunarsa ta cika duniya.
6Ubangiji ya halicci duniya da umarninsa,
Rana, da wata, da taurari kuma bisa ga maganarsa.
7Ya tattara tekuna wuri ɗaya.
Ya rurrufe zurfafan teku a ɗakunan ajiya.
8Bari duk duniya ta ji tsoron Ubangiji!
Ku ji tsoronsa ku mutanen duniya!
9Da magana ya halicci duniya,
Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana.
10Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al'umma,
Yakan hana su aikata shirye-shiryensu.
11Amma shirye-shiryensa sukan tabbata har abada.
Nufe-nufensa kuma dawwamammu ne har abada.
12Mai farin ciki ce al'ummar da Ubangiji yake Allahnta,
Masu farin ciki ne jama'ar da Ubangiji ya zaɓo wa kansa!
13Daga Sama Ubangiji ya dubo dukan 'yan adam.
14Daga inda yake mulki, yakan dubo dukan mazaunan duniya.
15Shi ya siffata tunaninsu, yana sane da dukan abin da suke yi.
16Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba,
Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba.
17Dawakan yaƙi ba su da amfani don cin nasara,
Ƙarfin nan nasu ba zai iya ceto ba.
18Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa,
Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa.
19Yakan cece su daga mutuwa,
Yakan rayar da su a lokacin yunwa.
20Ga Ubangiji muke sa zuciya,
Shi mai taimakonmu ne, mai kiyaye mu.
21Saboda da shi muke murna,
Muna dogara ga sunansa mai tsarki.
22Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji,
Da yake a gare ka muke sa zuciya.
Currently Selected:
Zab 33: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979