Bible App logo
Search Icon

Zab 31

31
Addu'ar Dogara ga Allah
1Na zo gare ka, ya Ubangiji, domin ka kiyaye ni.
Kada ka bari a yi nasara da ni.
Kai Allah mai adalci ne,
Ka cece ni, ina roƙonka!
2Ka ji ni! Ka cece ni yanzu!
Ka zama mafakata, don ka kiyaye ni,
Ka zama mai kāre ni, don ka cece ni.
3Kai ne mafakata da kariyata,
Ka bi da ni yadda ka alkawarta.
4Ka kiyaye ni daga tarkon da aka kafa domina,
Kai ne inuwata.
5 # Luk 23.46 Ina ba da kaina gare ka domin ka kiyaye ni.
Za ka fanshe ni, ya Ubangiji,
Kai Allah mai aminci ne.
6Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada,
Amma ni na dogara gare ka.
7Zan yi murna da farin ciki,
Saboda madawwamiyar ƙaunarka.
Ka ga wahalata,
Ka kuwa san damuwata.
8Ba ka bar magabtana su kama ni ba,
Ka kiyaye ni.
9Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,
Gama ina shan wahala,
Idanuna sun gaji saboda yawan kuka,
Na kuwa tafke ƙwarai!
10Baƙin ciki ya gajerta kwanakina,
Kuka kuma ya rage shekaruna.
Na raunana saboda yawan wahalata,
Har ƙasusuwana suna zozayewa!
11Magabtana duka suna mini ba'a,
Maƙwabtana sun raina ni,
Waɗanda suka san ni kuwa suna jin tsorona,
Sa'ad da suka gan ni a kan titi sukan guje mini.
12Duk an manta da ni kamar matacce,
Na zama kamar abin da aka jefar.
13Na ji magabtana da yawa suna raɗa,
Razana ta kewaye ni!
Suna ƙulla maƙarƙashiya don su kashe ni.
14Amma a gare ka na dogara, ya Ubangiji,
Kai ne Allahna.
15Kana lura da ni kullum,
Ka cece ni daga magabtana,
Daga waɗanda suke tsananta mini.
16Ni, bawanka ne,
Ka dube ni da alherinka,
Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!
17Ina kira gare ka, ya Ubangiji,
Kada ka bari a ci nasara a kaina!
Ka sa a ci nasara a kan mugaye,
Ka sa su yi shiru a lahira.
18Ka rufe bakin maƙaryatan can
Dukan masu girmankai da masu fāriya,
Waɗanda suke wa adalai maganar raini!
19Abin al'ajabi ne irin tanadin da ka yi wa masu tsoronka!
Abin da kake aikatawa a gaban kowa kuma,
Yana da banmamaki.
Kana kiyaye waɗanda suke amincewa da kai.
20Ka ɓoye su a wurinka lafiya daga makircin mutane,
A inuwa mai lafiya ka ɓoye su daga zargin magabtansu.
21Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Gama ya nuna mini ƙaunarsa mai ban al'ajabi,
Sa'ad da aka kewaye ni, aka fāɗa mini!
22Na ji tsoro, na zaci ka jefar da ni ne daga gabanka.
Amma ka ji kukana sa'ad da na yi kira gare ka neman taimako.
23Ku ƙaunaci Ubangiji, ku amintattun jama'arsa duka!
Ubangiji yana kiyaye masu aminci,
Amma yakan hukunta masu girmankai da tsanani.
24Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali,
Dukanku da kuke sa zuciya ga Ubangiji!

Currently Selected:

Zab 31: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in