Zab 18
18
Waƙar Dawuda ta Nasara
(2Sam 22.1-51)
1Ina ƙaunarka ƙwarai, ya Ubangiji!
Kai ne mai kāre ni.
2Ubangiji ne Mai Cetona,
Shi ne garkuwata mai ƙarfi.
Allahna, shi ne yake kiyaye ni,
Lafiya nake sa'ad da nake tare da shi,
Yana kiyaye ni kamar garkuwa,
Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.
3Na yi kira ga Ubangiji,
Yakan cece ni daga magabtana,
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
4Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,
Halaka ta auko mini a kai a kai.
5Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,
Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
6A shan wahalata na kira ga Ubangiji,
Na yi kira ga Allahna domin neman taimako.
A Haikalinsa ya ji muryata,
Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
7Sai duniya ta raurawa ta girgiza,
Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgiza
Saboda Allah ya husata!
8Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa,
Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.
9Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,
Tare da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.
10Ya sauko ta bisa bayan kerubobi,
Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.
11Ya rufe kansa da duhu,
Gizagizai masu duhu cike da ruwa, suna kewaye da shi.
12Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko
Daga cikin walƙiya da take gabansa,
Suka keto ta cikin gizagizai masu duhu.
13Sa'an nan Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama,
Aka ji muryar Maɗaukaki.
Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko.
14Ya harba kibansa, ya watsa magabtana,
Da walƙatawar walƙiya ya kore su.
15Kashiyar teku ta bayyana,
Tussan duniya sun bayyana,
Sa'ad da ka tsauta wa magabtana, ya Ubangiji,
Sa'ad da kuma ka yi musu tsawa da fushi.
16Ubangiji ya miƙa hannunsa daga samaniya ya ɗauke ni,
Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi.
17Ya cece ni daga magabtana masu ƙarfi,
Daga kuma dukan masu ƙina,
Gama sun fi ƙarfina!
18Sa'ad da nake shan wahala suka auka mini,
Amma Ubangiji ya kiyaye ni.
19Ya fisshe ni daga cikin hatsari,
Ya cece ni, don yana jin daɗina.
20Ubangiji yakan sāka mini, saboda ni adali ne,
Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne.
21Na yi biyayya da umarnan Ubangiji,
Ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba.
22Na kiyaye dukan dokokinsa,
Ban yi rashin biyayya da umarnansa ba.
23Ya sani ba ni da laifi,
Domin na kiyaye kaina daga mugunta.
24Don haka ya sāka mini, domin ni adali ne,
Gama ya sani ni marar laifi ne.
25Kai, ya Ubangiji, mai aminci ne ga masu aminci,
Kai nagari ne, cikakke ga kamilai.
26Kai Mai Tsarki ne ga waɗanda suke tsarkaka,
Amma kana gāba da mugaye.
27Kakan ceci masu tawali'u,
Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.
28Ubangiji yakan ba ni haske,
Allah yakan kawar da duhuna.
29Yakan ba ni ƙarfin da zan fāɗa wa magabtana,
Da ikon rinjayar kagararsu.
30Wannan Allah dai! Ayyukansa kamiltattu ne ƙwarai,
Maganarsa abar dogara ce!
Kamar garkuwa yake, ga duk mai neman taimako a wurinsa.
31Ubangiji shi kaɗai ne Allah,
Allah ne kaɗai kāriyamu.
32Shi ne Allahn da yake ƙarfafa ni,
Yana kiyaye lafiyata a kan hanya.
33 #
Hab 3.19
Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa.
Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.
34Yakan horar da ni don yaƙi,
Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.
35Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni,
Na zama babban mutum saboda kana lura da ni,
Ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.
36Ka tsare ni, ba a kama ni ba,
Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.
37Na kori magabtana, har na kama su,
Ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su.
38Zan buge su har ƙasa, ba kuwa za su tashi ba,
Za su fāɗi ƙarƙashin ƙafafuna.
39Kakan ba ni ƙarfin yin yaƙi,
Kakan ba ni nasara a kan magabtana.
40Ka kori magabtana daga gare ni,
Zan hallaka waɗanda suke ƙina.
41Suna kukan neman taimako, amma ba wanda zai iya cetonsu,
Za su yi kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa ba.
42Zan murƙushe su har su zama ƙura
Wadda iska take kwashewa,
Zan tattake su kamar caɓi a titi.
43Ka cece ni daga mutane masu tawaye,
Ka naɗa ni in yi mulkin sauran al'umma,
Jama'ar da ban san ta ba, ta zama abin mulkina.
44Za su yi biyayya sa'ad da suka ji ni,
Baƙi za su rusuna mini,
45Za su karai,
Su fita, suna rawar jiki daga kagaransu.
46Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai kāre ni!
Allah ne, Mai Cetona! A yi shelar girmansa!
47Yakan ba ni nasara a kan magabtana,
Yakan sa jama'a a ƙarƙashina,
48Yakan cece ni daga maƙiyana.
Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji,
Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya,
49 #
Rom 15.9
Don haka zan yabe ka a cikin al'ummai,
Zan raira maka yabo.
50Kullayaumi Allah yakan ba sarkin da ya naɗa babbar nasara.
Yakan nuna madawwamiyar ƙauna ga wanda ya zaɓa,
Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.
Currently Selected:
Zab 18: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979