Zab 13
13
Addu'ar Neman Taimako daga Wahala
1Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji?
Har abada ne?
Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka?
2Har yaushe raina zai jure da shan wahala?
Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana?
Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina?
3Ka dube ni, ya Ubangiji Allahna, ka amsa mini,
Ka mayar mini da ƙarfina, don kada in mutu.
4Sa'an nan maƙiyana ba za su ce, “Ai, mun yi nasara da shi” ba!
Ba za su iya yin murna saboda fāɗuwata ba.
5Amma ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarka,
Zan yi murna gama za ka cece ni.
6Zan raira waƙa ga Ubangiji,
Gama ya kyautata mini.
Currently Selected:
Zab 13: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979