Zab 115
115
Allah Mai Gaskiya Makaɗaici
1A gare ka kaɗai, ya Ubangiji,
A gare ka kaɗai, ba a gare mu ba,
Dole a girmama ka,
Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.
2Me ya sa sauran al'umma suke tambayarmu,
“Ina Allahnku?”
3Allahnmu yana Sama,
Yana aikata yadda yake so.
4 #
Zab 135.15-18; W.Yah 9.20 Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne,
Da hannu aka siffata su.
5Suna da baki, amma ba sa magana,
Suna da idanu, amma ba sa gani.
6Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,
Suna da hanci, amma ba sa jin ƙanshi.
7Suna da hannuwa, amma ba sa iya riƙon kome,
Suna da ƙafafu, amma ba sa iya tafiya.
Ba su da murya sam.
8Ka sa waɗanda suka yi su,
Da dukan masu dogara gare su,
Su zama kamar gumakan da suka yi!
9Ku dogara ga Ubangiji, ya ku jama'ar Isra'ila!
Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.
10Ku dogara ga Ubangiji, ya ku firistoci na Allah!
Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.
11Ku dogara ga Ubangiji, dukanku waɗanda kuke tsoronsa!
Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.
12Ubangiji yana tuna da mu, zai kuwa sa mana albarka,
Zai sa wa jama'ar Isra'ila albarka,
Da dukan firistoci na Allah.
13 #
W.Yah 11.18; 19.5 Zai sa wa dukan waɗanda suke tsoronsa albarka.
Babba da yaro.
14Ubangiji ya ba ku 'ya'ya,
Ku da zuriyarku.
15Ubangiji, wanda ya yi sama da ƙasa
Ya sa muku albarka!
16Samaniya ta Ubangiji ce kaɗai,
Amma ya ba mutane duniya.
17Matacce ba ya yabon Ubangiji,
Ko wanda ya gangara zuwa cikin kabari.
18Amma mu da muke rayayyu, za mu yi masa godiya.
A yanzu da har abada.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Currently Selected:
Zab 115: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979