Zab 114
114
Waƙar Idin Ƙetarewa
1 #
Fit 12.51
Sa'ad da jama'ar Isra'ila suka bar Masar,
Sa'ad da zuriyar Yakubu suka bar baƙuwar ƙasar nan,
2Yahuza ya zama tsattsarkar jama'ar Ubangiji,
Isra'ila ya zama abin mallakarsa.
3 #
Fit 14.21;
Josh 3.16
Bahar Maliya da ya duba, sai ya gudu,
Kogin Urdun ya daina gudu.
4Duwatsu suka yi ta tsalle kamar awaki,
Tuddai kuwa suka yi ta tsalle suna kewayawa kamar tumaki.
5Me ya faru ne, ya teku, da ya sa ki gudu?
Kai fa Urdun, me ya sa ka daina gudu?
6Ku fa duwatsu, me ya sa kuka yi ta tsalle kamar awaki?
Tuddai, me ya sa kuka yi ta tsalle,
Kuna kewayawa kamar tumaki?
7Ki yi rawar jiki, ya ke duniya,
Saboda zuwan Ubangiji,
A gaban Allah na Yakubu,
8 #
Fit 17.1-7; L.Ƙid 20.2-13 Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa,
Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai,
Masu bulbulo da ruwa.
Currently Selected:
Zab 114: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979