YouVersion Logo
Search Icon

K.Mag 7

7
Wayon Mazinaciya
1Ɗana, ka tuna da abin da na faɗa, kada ka manta da abin da na ce maka ka yi. 2Ka yi abin da na faɗa maka, za ka rayu. Ka natsu, ka bi koyarwata, ka tsare ta kamar ƙwayar idonka. 3Kullayaumi ka riƙe koyarwata tare da kai, ka rubuta ta a zuciyarka. 4Ka mai da hikima 'yar'uwarka, basira kuwa ta zama ƙawarka ta jikinka. 5Za su nisanta ka da matan mutane, daga kuma mata masu maganganun alfasha.
6Wata rana ina leƙawa ta tagar ɗakina, 7sai na ga waɗansu samari masu yawa waɗanda ba su gogu da duniya ba, musamman sai na lura da wani dolo a cikinsu. 8Yana tafe a kan titi kusa da kusurwar da take a zaune, yana wucewa kusa da gidanta, 9da magariba cikin duhu. 10Sai ta tarye shi, ta ci ado kamar karuwa, tana shirya yadda za ta yaudare shi. 11(Ba ta jin tsoro, ba ta kuma jin kunya, ko yaushe tana ta gantali a tituna. 12Takan tsaya tana jira a kowace kusurwa, wani lokaci a tituna, wani lokaci kuma a kasuwa.) 13Ta rungumi saurayin, ta sumbace shi, ta dubi tsabar idonsa ta ce, 14“Na miƙa hadayu yau, ina da nama na hadayu. 15Shi ya sa na fito ina nemanka, ina so in gan ka, ga shi kuwa, na gan ka! 16Na lulluɓe gadona da zannuwan lilin masu launi iri iri daga Masar. 17Na yayyafa musu turaren mur da na aloyes da na kirfa. 18Ka zo mu sha daɗin ƙauna, mu more dukan dare, mu yi farin ciki rungume da juna. 19Mijina ba ya gida, ya yi tafiya mai nisa. 20Ya tafi da kuɗi masu yawa, ba zai komo ba sai bayan mako biyu.” 21Ta jarabce shi da kwarkwasarta, sai ya ba da kai ga daɗin bakinta. 22Nan da nan ya bi ta kamar sā zuwa mayanka, kamar barewa tana tsalle zuwa cikin tarko, 23inda kibiya za ta soke zuciyarta. Yana kama da tsuntsun da yake zuwa cikin tarko, bai kuwa sani ransa yana cikin hatsari ba.
24Yanzu fa 'ya'yana, ku kasa kunne gare ni, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa. 25Kada ku yarda irin wannan mace ta rinjayi zuciyarku, kada ku yi ta yawon nemanta. 26Ita ce sanadin hallakar mutane da yawa, ta sa mutane da yawa mutuwa, har ba su ƙidayuwa. 27Tafiya gidanta kuna kan hanya zuwa mutuwa ke nan, gajeruwar hanya ce zuwa lahira.

Currently Selected:

K.Mag 7: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in