K.Mag 6
6
Faɗakarwa a kan Ragwanci da Ƙarya
1Ɗana, ka taɓa yin alkawari ka ɗaukar wa wani lamuni? 2Maganganunka sun taɓa kama ka, ko alkawaranka sun taɓa zamar maka tarko? 3To, ɗana, kana cikin ikon wannan mutum, amma ga yadda za ka yi ka fita, sheƙa zuwa wurinsa, ka roƙe shi ya sake ka. 4Kada ka yarda ka yi barci ko ka huta. 5Ka fita daga cikin tarkon kamar tsuntsu ko barewar da ta tsere wa maharbi.
6Bari ragwaye su yi koyi da tururuwa. 7Ba su da shugaba, ba su da sarki, ko mai mulki, 8amma da kaka sukan tanada wa kansu abinci, domin kwanakin bazara. 9Har yaushe rago zai yi ta ɓalɓalcewa? Yaushe zai farka? 10#K.Mag 24.33,34 Yakan ce, “Bari in ɗan ruruma, in naɗa hannuwana in shaƙata.” 11Amma lokacin da yake sharar barci, tsiya za ta auka masa kamar ɗan fashi da makamai.
12Sakarkari, wato mugaye sukan yi ta baza jita-jita. 13Sukan yi ƙyifce, ko su yi nuni don su yaudare ka. 14A kowane lokaci suna shirya mugunta a kangararren hankalinsu, suna kuta tashin hankali ko'ina. 15Saboda wannan masifa za ta fāɗa musu farat ɗaya ba makawa, za a yi musu mummunan raini.
16-19Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba,
duban raini,
harshe mai faɗar ƙarya,
hannuwan da suke kashe marasa laifi,
kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru,
mutum mai gaggawar aikata mugunta,
mai yawan shaidar zur,
mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.
Faɗakarwa a kan Zina
20Ɗana, ka yi abin da mahaifinka ya faɗa maka, kada ka manta da koyarwar mahaifiyarka. 21Kullum ka kiyaye abin da suke faɗa maka, ka kulle su kuma a zuciyarka. 22Koyarwarsu za ta bi da kai sa'ad da kake tafiya, ta kiyaye ka da dare, ta kuma ba ka shawara da rana. 23Doka da abubuwan da take koyarwa haske ne mai haskakawa. Tsautawa tana iya koya maka zaman duniya. 24Za ta tsare ka daga mugayen mata, daga kalmomin alfasha da suke fitowa daga bakin matan waɗansu. 25Kada kyansu ya jarabce ka, kada ka faɗa cikin tarkon feleƙensu. 26Mutum ta dalilin karuwa zai sha hasarar abin da ya mallaka duka ta wurin zina.
27Ka iya rungumar wuta a ƙirjinka sa'an nan ka ce ba za ta ƙone tufafinka ba? 28Ka iya tafiya a kan garwashi sa'an nan ka ce ƙafafunka ba za su ƙone ba? 29Haka yake da mutumin da ya kwana da matar wani. Duk wanda ya aikata wannan, zai sha wahala. 30Mutane ba sukan raina wanda ya saci abinci don yana jin yunwa ba, 31duk da haka in an kama shi, sai ya biya diyya sau bakwai, tilas kuwa ya ba da dukan abin da yake da shi. 32Amma mazinaci marar hankali ne, gama hallaka kansa yake yi. 33Zai sha dūka, a wulakanta shi, zai dawwama cikin kunya. 34Hasalar miji mai kishi babu irinta, ramawarsa ba dama. 35Ba zai karɓi biya ba, ba kyautar da za a yi masa wadda za ta kwantar da fushinsa.
Currently Selected:
K.Mag 6: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979