YouVersion Logo
Search Icon

L.Ƙid 33

33
Tafe-tafe daga Masar zuwa Mowab
1Waɗannan su ne wuraren da Isra'ilawa suka yi zango sa'ad da suka fita runduna runduna daga ƙasar Masar ta hannun Musa da Haruna. 2Bisa ga faɗar Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tashinsu da wuraren saukarsu. Wuraren saukarsu da na tashinsu ke nan.
3Sun tashi daga Ramases a rana ta goma sha biyar ga watan fari. A kashegarin Idin Ƙetarewa ne suka fita gabagaɗi a gaban dukan Masarawa. 4Masarawa suna ta binne gawawwakin 'ya'yan farinsu da Ubangiji ya karkashe musu. Banda 'ya'yan farinsu kuma Ubangiji ya hukunta wa allolinsu.
5Isra'ilawa kuwa suka tashi daga Ramases suka sauka a Sukkot. 6Suka tashi daga Sukkot suka sauka a Etam wadda take a gefen jejin. 7Da suka tashi daga Etam, sai suka juya zuwa Fi-hahirot wadda take gaban Ba'al-zefon suka sauka a gaban Migdol. 8Da suka tashi daga gaban Fi-hahirot sai suka haye teku zuwa cikin jejin. Suka yi tafiya kwana uku a jejin Etam, suka sauka a Mara. 9Suka tashi daga Mara suka zo Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa guda goma sha biyu da itacen dabino guda saba'in. Sai suka sauka a can.
10Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya. 11Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin. 12Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka. 13Daga Dofka suka tafi Alush. 14Suka tashi daga Alush suka sauka a Refidim inda mutane suka rasa ruwan sha.
15Suka tashi daga Refidim suka sauka a jejin Sinai. 16Da suka tashi daga jejin Sinai, sai suka sauka a Kibrot-hata'awa. 17Suka tashi daga Kibrot-hata'awa suka sauka a Hazerot. 18Da suka tashi daga Hazerot, sai suka sauka a Ritma. 19Suka tashi daga Ritma suka sauka a Rimmon-farez. 20Suka tashi daga Rimmon-farez, suka sauka a Libna. 21Da suka tashi daga Libna, sai suka sauka a Rissa. 22Da suka tashi daga Rissa, suka sauka a Kehelata. 23Suka tashi daga Kehelata suka sauka a Dutsen Shifer. 24Suka tashi daga Dutsen Shifer suka sauka a Harada. 25Da suka tashi daga Harada, suka sauka a Makelot. 26Suka tashi daga Makelot suka sauka a Tahat. 27Suka tashi daga Tahat suka sauka a Tara. 28Suka kama hanya daga Tara suka sauka a Mitka. 29Suka kuma kama hanya daga Mitka suka sauka a Hashmona. 30Daga Hashmona suka sauka a Moserot. 31Da suka tashi daga Moserot suka sauka a Bene-ya'akan. 32Suka tashi daga Bene-ya'akan suka sauka a Hor-hagidgad. 33Da suka tashi daga Hor-hagidgad suka sauka a Yotbata. 34Suka kama hanya daga Yotbata suka sauka a Abrona. 35Da suka tashi daga Abrona, sai suka sauka a Eziyon-geber. 36Suka tashi daga Eziyon-geber suka sauka a jejin Zin, wato Kadesh. 37Da suka kama hanya daga Kadesh suka sauka a Dutsen Hor a kan iyakar ƙasar Edom.
38 # L.Ƙid 20.22-28; M.Sh 10.6; 32.50 Bisa ga umarnin Ubangiji, Haruna firist ya hau Dutsen Hor inda ya rasu a rana ta fari ga watan biyar a shekara ta arba'in ta fitowar jama'ar Isra'ila daga ƙasar Masar. 39Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku sa'ad da ya rasu a Dutsen Hor.
40 # L.Ƙid 21.1 Sai Sarkin Arad, Bakan'ane wanda yake zaune a Negeb, a ƙasar Kan'ana, ya ji zuwan Isra'ilawa.
41Isra'ilawa kuma suka tashi daga Dutsen Hor, suka sauka a Zalmona. 42Daga Zalamona suka sauka a Funon. 43Da suka tashi daga Funon, sai suka sauka a Obot. 44Suka kuma kama hanya daga Obot suka sauka a Abarim a karkarar Mowab. 45Suka tashi daga nan suka sauka a Dibon-gad. 46Suka tashi daga Dibon-gad suka sauka a Almon-diblatayim. 47Da suka tashi daga Almon-diblatayim, suka sauka a duwatsun Abarim a gaban Nebo. 48Daga duwatsun Abarim suka sauka a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko. 49Suka sauka kusa da Urdun, suka kakkafa alfarwansu tun daga Betyeshimot har zuwa Abel-shittim, a filayen Mowab.
Umarni kafin su Haye Urdun
50Sai Ubangiji ya yi magana da Musa a filayen Mowab kusa da Urdun, daura da Yariko, ya ce 51ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, “Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa ƙasar Kan'ana, 52sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu. 53Sa'an nan ku mallaki ƙasar, ku zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta. 54#L.Ƙid 26.54-56Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar. 55Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi. 56Idan ba ku kore su ba, zan lalatar daku kamar yadda na shirya lalatar da su.”

Currently Selected:

L.Ƙid 33: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for L.Ƙid 33