YouVersion Logo
Search Icon

L.Ƙid 32

32
Kabilai a Gabashin Urdun
(M.Sh 3.12-22)
1Kabilan Ra'ubainu da Gad suna da dabbobi da yawa ƙwarai. Da suka ga ƙasar Yazar da ta Gileyad wuri ne mai kyau domin shanu, 2sai suka je wurin Musa da Ele'azara firist, da shugabannin taron jama'ar, 3suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba'al-meyon, 4ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban taron jama'a, ƙasa ce mai kyau don dabbobi. Ga shi kuwa, barorinka suna da dabbobi da yawa. 5Idan mun sami tagomashi a gare ka, ka ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu, kada ka kai mu a wancan hayin Urdun.”
6Amma Musa ya amsa musu ya ce, “Wato sai 'yan'uwanku su yi ta yaƙi, ku kuwa ku yi zamanku a nan, ko? 7Don me za ku karya zuciyar jama'ar Isra'ila daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su? 8#L.Ƙid 13.17-33Haka iyayenku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh-barneya don su dubo ƙasar. 9Gama sa'ad da suka tafi Kwarin Eshkol suka ga ƙasar, suka karya zuciyar jama'a daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su. 10#L.Ƙid 14.26-35Saboda haka Ubangiji ya husata a ranan nan, har ya yi wa'adi ya ce, 11‘Hakika ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, domin ba su bi ni sosai ba. 12Sai dai Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, da Joshuwa ɗan Nun, domin su ne kaɗai suka bi ni sosai.’ 13Saboda Ubangiji ya husata da isra'ilawa, shi ya sa suka yi ta yawo a jeji har shekara arba'in, wato sai da tsaran nan wadda ta aikata mugunta a gaban Ubangiji ta ƙare. 14Ga shi, ku kuma da kuke 'ya'yan mugayen mutanen nan, ku da kuke a matsayin iyayenku, kuna so ku ƙara sa Ubangiji ya husata da Isra'ilawa. 15Gama idan kun ƙi binsa, zai sāke yashe ku a jeji. Ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakar mutanen nan duka.”
16Sai suka zo kusa da shi, suka ce, “Za mu gina garu na dutse don mu kāre dabbobinmu, da birane don 'ya'yanmu a nan. 17'Ya'yanmu za su zauna a biranen don gudun mazaunan ƙasar, amma mu za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra'ilawa, har mu kai su wuraren zamansu. 18Ba kuwa za mu koma gidajenmu ba, sai lokacin da kowane Ba'isra'ile ya sami gādonsa. 19Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.”
20Sai Musa ya ce musu, “Idan za ku yi haka, wato ku ɗauki makamai, ku tafi yaƙi a gaban Ubangiji, 21kowane sojanku ya haye Urdun a gaban Ubangiji, har lokacin da Ubangiji ya kori abokan gābansa daga gabansa, 22har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama'ar Isra'ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji. 23Idan kuwa ba ku yi haka ba, kun yi wa Ubangiji laifi, ku tabbata fa alhakin zunubinku zai kama ku. 24To, sai ku gina wa 'ya'yanku birane, ku gina wa garkunanku garu, amma ku aikata abin da kuka faɗa da bakinku.”
25Sai Gadawa da Ra'ubainawa suka amsa wa Musa, suka ce, “Barorinka za su yi kamar yadda ka umarta. 26'Ya'yanmu, da matanmu, da tumakinmu, da shanunmu za su zauna a birane a nan Gileyad. 27Amma kowane soja a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji zuwa yaƙi kamar yadda shugabanmu ya faɗa.”
28 # Josh 1.12-15 Sai Musa ya yi wa Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra'ila kashedi a kansu, 29ya ce, “Idan kowane soja na Gadawa da Ra'ubainawa zai haye Urdun tare da ku don yaƙi har an ci ƙasar dominku, to, sai ku ba su ƙasar Gileyad ta zama mallakarsu. 30Amma idan ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo tare da ku a cikin ƙasar Kan'aniyawa.”
31Gadawa da Ra'ubainawa kuwa suka ce, “Kamar yadda Ubangiji ya ce wa barorinka, haka za mu yi. 32Za mu haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa cikin ƙasar Kan'aniyawa, amma za mu sami gādonmu a wannan hayin Urdun.”
33Sa'an nan Musa ya ba Gadawa, da Ra'ubainawa, da rabin mutanen Manassa, ɗan Yusufu, mulkin Sihon, Sarkin Amoriyawa, da mulkin Og, Sarkin Bashan, wato ƙasar da biranenta da karkaransu. 34Sai Gadawa suka gina Dibon, da Atarot, da Arower, 35da Atarot-shofan, da Yazar, da Yogbeha, 36da Bet-nimra, da Bet-aram su zama birane masu garu da shinge don dabbobi. 37Ra'ubainawa kuwa suka gina Heshbon da Eleyale, da Kiriyatayim, 38da Nebo, da Ba'al-meyon, da Sibma.
39Mutanen Makir, ɗan Manassa, suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori Amoriyawan da suke cikinta. 40Sai Musa ya ba mutanen Makir, ɗan Manassa, Gileyad, suka zauna ciki. 41Yayir, ɗan Manassa, ya tafi ya ci ƙauyukansu da yaƙi, suka ba su suna Hawot-yayir. 42Noba kuma ya tafi ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya ba ta suna Noba bisa ga sunansa.

Currently Selected:

L.Ƙid 32: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in