L.Ƙid 22
22
Balak ya Sa a Kirawo masa Bal'amu
1Isra'ilawa suka kama tafiya, suka yi zango a filayen Mowab a hayin Urdun daura da Yariko.
2Balak ɗan Ziffor ya ga abin da Isra'ilawa suka yi wa Amoriyawa. 3Sai Mowabawa suka firgita ƙwarai saboda yawan mutanen. Tsoron Isra'ilawa ya kama su. 4Mowabawa kuwa suka ce wa dattawan Madayanawa, “Yanzun nan wannan taro zai lashe dukan abin da yake kewaye da mu kamar yadda sā yakan lashe ciyawar saura.” Don haka Balak ɗan Ziffor wanda yake sarautar Mowab a lokacin, 5#L.Ƙid 31.8; 2Bit 2.15,16; Yahu 1.11ya aiki manzanni zuwa wurin Bal'amu ɗan Beyor a Fetor, a ƙasar danginsa, wadda take kusa da kogin, su kirawo shi, su ce, “Ga mutane sun fito daga ƙasar Masar, sun mamaye ƙasar, ga shi, suna zaune daura da ni. 6Ina roƙonka, ka zo yanzu, ka la'anta mini mutanen nan, gama sun fi ƙarfina, ko ya yiwu in ci su, in kore su daga ƙasar, gama na sani duk wanda ka sa wa albarka zai albarkatu, wanda kuwa ka la'anta, zai la'antu.”
7Dattawan Mowab da na Madayana suka ɗauki kafin alkalami suka tafi wurin Bal'amu suka faɗa masa saƙon Balak. 8Ya ce musu, “Ku kwana a nan, ni kuwa zan shaida muku abin da Ubangiji zai faɗa mini.” Sai dattawan Mowab suka zauna wurin Bal'amu.
9Allah kuwa ya zo wurin Bal'amu ya ce masa, “Suwane ne mutanen da suke tare da kai?”
10Sai Bal'amu ya ce wa Allah, “Ai, Balak ne ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya aiko ya ce mini, 11‘Ga jama'a sun fito daga Masar, sun mamaye ƙasar, ka zo, ka la'anta mini su, watakila zan iya yin yaƙi da su, in kore su!’ ”
12Allah kuwa ya ce wa Bal'amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la'anta su ba, gama albarkatattu ne su.”
13Da safe Bal'amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.” 14Domin haka dattawan Mowab suka tashi, suka koma wurin Balak, suka ce masa, “Bal'amu bai yarda ya biyo mu ba.”
15Sai Balak ya sāke aiken dattawa da yawa masu daraja fiye da na dā. 16Suka je wurin Bal'amu, suka ce masa, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, ‘Kada ka bar wani abu ya hana ka zuwa wurina, 17gama zan ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mini in yi, zan yi, ka zo ka la'anta mini wannan jama'a.’ ”
18Amma Bal'amu ya amsa ya ce wa barorin Balak, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba. 19Amma ina roƙonku ku kwana a nan yau har in san abin da Ubangiji zai faɗa mini.”
20Sal Allah ya je wurin Bal'amu da dare, ya ce masa, “Idan mutanen nan sun zo kiranka ne, sai ka tashi, ka tafi tare da su, amma abin da na umarce ka kaɗai za ka yi.”
Mala'ika da Jakar Bal'amu
21Da safe sai Bal'amu ya tashi ya yi wa jakarsa shimfiɗa, ya tafi tare da dattawan Mowab. 22Allah kuwa ya husata don ya tafi, mala'ikan Ubangiji ya tsaya a hanya ya tarye shi. Shi kuwa yana tafe a bisa jakarsa tare da barorinsa biyu. 23Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga saura. Bal'amu kuwa ya buge ta don ya komar da ita a hanyar. 24Sai mala'ikan Ubangiji ya je, ya tsaya a inda hanyar ta yi matsatsi a tsakanin bangayen gonakin inabi. 25Sa'ad da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, ta matsa a jikin bango, ta goge ƙafar Bal'amu ga bangon, sai ya sāke bugunta. 26Mala'ikan Ubangiji kuma ya sha kanta, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu. 27Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙafafun Bal'amu. Sai Bal'amu ya husata, ya bugi jakar da sandansa. 28Ubangiji kuwa ya buɗe bakin jakar, ta ce wa Bal'amu, “Me na yi maka, da ka buge ni har sau uku?”
29Bal'amu ya ce mata, “Domin kin shashantar da ni, da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki.”
30Sai jakar ta ce wa Bal'amu, “Ba ni ce jakarka ba wadda kake ta hawa dukan lokacin nan har zuwa yau? Na taɓa yi maka haka?”
Ya ce, “A'a.”
31Ubangiji kuwa ya buɗe idanun Bal'amu, ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye a hanya da takobi zāre a hannunsa. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki. 32Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ce masa, “Me ya sa ka bugi jakarka har sau uku? Na fito ne don inhana ka, gama hanyarka ba daidai ba ce a gabana. 33Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da ba ta kakuce mini ba, lalle da na kashe ka, in bar ta da rai.”
34Sai Bal'amu ya ce wa mala'ikan Ubangiji, “Na yi zunubi, gama ban sa ka tsaya a hanya don ka tarye ni ba. Yanzu fa, idan ka ga mugun abu ne, to, sai in koma.”
35Ubangiji kuwa ya ce wa Bal'amu, “Tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka shi kaɗai za ka faɗa.” Sai Bal'amu ya tafi tare da dattawan Balak.
Balak ya Marabci Bal'amu
36Sa'ad da Balak ya ji Bal'amu ya zo, sai ya fito ya tarye shi a Ar, wato wani birni a bakin Kogin Arnon, a kan iyakar Mowab. 37Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Me ya sa ba ka zo wurina ba, sai yanzu? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?”
38Bal'amu ya amsa wa Balak ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu! Ina da wani ikon yin wata magana ne? Maganar da Allah ya sa a bakina, ita zan faɗa, tilas.” 39Sai Bal'amu ya tafi tare da Balak suka je Kiriyat-huzot. 40Can Balak ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bal'amu da dattawan da suke tare da shi.
41Kashegari, sai Balak ya ɗauki Bal'amu ya kai shi kan Bamotba'al, daga can ya ga rubu'in mutanen.
Currently Selected:
L.Ƙid 22: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979