L.Ƙid 15
15
Ka'idodin Yin Hadayu
1Ubangiji ya ba Musa 2waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa su kiyaye su a ƙasar da zai ba su. 3Sa'ad da za su yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji daga cikin garken shanu, ko na tumaki da awaki, ko hadaya ta ƙonawa ce, ko ta cika wa'adi ce, ko ta yardar rai ce, ko ta ƙayyadaddun idodinsu ce, don a ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, 4sai shi wanda ya kawo hadayar ga Ubangiji, ya kuma kawo hadaya ta gari, humushin garwa guda kwaɓaɓɓe da rubu'in moɗa na mai. 5Ya kuma shirya hadaya ta sha, rubu'in moɗa ta ruwan inabi domin kowane ɗan rago na hadaya ta ƙonawa. 6Idan kuwa da rago ne, a shirya hadaya ta gari humushi biyu na garwa, a kwaɓa da sulusin moɗa na mai. 7Za a kuma miƙa hadaya ta sha da sulusin moɗa na ruwan inabi, don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 8Idan kuwa da bijimi ne za a yi hadaya ta ƙonawar, ko sadaka domin cika wa'adi, ko ta salama ga Ubangiji, 9sai a miƙa hadaya ta gari tare da bijimin, humushi uku na garwar gari kwaɓaɓɓe da rabin moɗa na mai. 10Za a kuma miƙa hadaya ta sha da rabin moɗa na ruwan inabi. Hadaya ce da akan yi da wuta, mai yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
11Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru. 12Bisa ga yawan abin da aka shirya, haka za a yi da kowannensu bisa ga adadinsu. 13Haka dukan waɗanda suke 'yan ƙasa za su yi in za su ba da hadayar da akan yi da wuta don yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 14Idan baƙon da yake baƙunci a cikinsu ko wane ne da yake tare da su a dukan zamanansu, yana so ya ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, sai ya yi kamar yadda suke yi. 15Ka'ida ɗaya ce domin taron jama'a da kuma baƙin da yake zaune tare da su. Ka'ida ce madawwamiya a dukan zamanansu. Kamar yadda suke a gaban Ubangiji, haka kuma baƙon da yake baƙunci a cikinsu yake. 16#L.Fir 24.22Ka'ida ɗaya ce umarni kuma ɗaya ne domin su da baƙin da yake baƙunci a cikinsu.
17Ubangiji ya ba Musa 18waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa su kiyaye a ƙasar da zai ba su. 19Sa'ad da suke cin amfaninta, sai su miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji. 20Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari sai su yi wainar da za su ɗaga don yin hadaya da amfanin masussuka. 21Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari, sai su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa a dukan zamanansu.
22Amma idan sun yi kuskure, ba su kiyaye dukan umarnan nan waɗanda Ubangiji ya faɗa wa Musa ba, 23wato duk dai abin da ubangiji ya umarta ta bakin Musa tun daga ranar da Ubangiji ya ba da umarnan, har zuwa dukan zamanansu, 24idan jama'a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka'idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi. 25Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama'ar Isra'ilawa, za a kuwa gafarta musu kuskuren, domin sun kawo hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi ga Ubangiji saboda kuskurensu. 26Za a gafarta wa dukan taron jama'ar Isra'ilawa da baƙon da yake baƙunci a cikinsu, kuskuren da suka yi.
27 #
L.Fir 4.27-31
Idan bisa ga kuskure wani mutum ya yi zunubi, sai ya ba da 'yar akuya bana ɗaya ta yin hadaya don zunubi. 28Firist kuwa zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin da ya yi kuskuren, gama ya yi zunubi ba da saninsa ba, za a kuwa gafarta masa. 29Ka'idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba'isra'ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu.
30Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi, 31gama ya raina maganar Ubangiji, ya karya umarninsa. Hakika za a kashe mutumin nan, alhakin zunubinsa, yana wuyansa.
Jajjefewar Wanda ya Ɓata Ranar Asabar
32Sa'ad da Isra'ilawa suke jeji, sai aka iske wani yana tattara itace a ranar Asabar. 33Sai suka kai shi wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'a. 34Aka sa shi a gidan waƙafi domin ba a bayyana abin da za a yi da shi ba tukuna. 35Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “A kashe mutumin, dukan taron jama'a za su jajjefe shi da duwatsu a bayan zangon.” 36Dukan taron jama'a suka kai shi bayan zangon, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Dokoki a kan Tuntayen Riguna
37Ubangiji ya umarci Musa ya ce, 38#M.Sh 22.12“Ka faɗa wa Isra'ilawa su yi wa shafin rigunansu tuntaye a dukan zamananku. A kan kowane tuntu, su sa shuɗin zare. 39Tuntu zai zama musu abin dubawa don su riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji su aikata su, don kada su bi son zuciyarsu, da sha'awar idanunsu yadda suka taɓa yi. 40Da haka za su riƙa tunawa, su aikata dukan umarnaina su zama tsarkakakku gare ni. 41Gama ni ne Ubangiji Allahnku, na fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
Currently Selected:
L.Ƙid 15: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979