L.Ƙid 14
14
Mutane suka yi Yaji
1Sai dukan taron jama'a suka yi kuka da babbar murya dukan dare saboda wahala. 2Dukan Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suke ce, “Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko kuwa a wannan jeji. 3Me ya sa Ubangiji ya kawo mu a wannan ƙasa, mu mutu da takobi? Matanmu da ƙanananmu za su zama ganima. Ba zai fi mana kyau, mu koma Masar ba?” 4Sai suka ce wa juna, “Bari mu shugabantar da wani, mu koma Masar.”
5Sa'an nan Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban dukan taron jama'ar Isra'ilawa. 6Sai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu. 7Suka ce wa dukan taron jama'ar Isra'ilawa, “Ƙasar da muka ratsa ta don mu leƙi asirinta, ƙasa ce mai kyau ƙwarai da gaske. 8Idan Ubangiji yana jin daɗinmu zai kai mu a wannan ƙasa da take cike da yalwar abinci, ya ba mu ita. 9#Ibr 3.16Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da suke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.” 10Amma taron jama'a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutanen Isra'ila daga cikin alfarwa ta sujada.
11Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su raina ni? Har yaushe za su ƙi gaskata ni, ko da yake na aikata alamu a tsakiyarsu? 12Zan kashe su da annoba, in raba su da gādonsu. Zan yi wata al'umma da kai, wadda za ta fi su girma da iko.”
13 #
Fit 32.11-14
Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji, gama ka fitar da mutanen daga cikinsu da ƙarfin ikonka. 14Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama'ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al'amudin wuta. 15Idan kuwa ka kashe jama'ar nan gaba ɗaya, sai al'umman da suka ji labarinka, su ce, 16‘Domin Ubangiji ya kāsa kai jama'ar nan zuwa cikin ƙasar da ya rantse zai ba su, don haka ya kashe su a cikin jeji.’ 17Yanzu fa, ya Ubangiji, ina roƙonka ka sa ikonka ya zama da girma kamar yadda ka alkawarta cewa, 18#Fit 20.5,6; 34.6,7; M.Sh 5.9,10; 7.9,10‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa 'ya'ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’ 19Ina roƙonka ka gafarta muguntar wannan jama'a saboda ƙaunarka mai girma, kamar yadda kake gafarta musu tun daga Masar har zuwa yanzu.”
20Sai Ubangiji ya ce, “Saboda maganarka na gafarta. 21#Ibr 3.18Amma, hakika, na rantse da zatina, kamar yadda ɗaukakata za ta cika duniya duka, 22dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba, 23ba za su ga ƙasar da na rantse zan ba kakanninsu ba. Duk waɗanda suka raina ni, ba za su ga ƙasar ba, 24#Josh 14.9-12sai dai bawana Kalibu da yake ruhunsa dabam ne, gama ya bi ni sosai. 25Yanzu fa, tun da yake Amalekawa da Kan'aniyawa suna zaune a kwarin, gobe sai ku juya ku nufi wajen jejin ta hanyar Bahar Maliya.”
Ubangiji ya Hukunta Jama'ar saboda Gunaguni
(M.Sh 1.34-40)
26Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna, 27“Har yaushe wannan mugun taron jama'a zai yi ta gunaguni a kaina? Na ji gunagunin da Isra'ilawa suka yi a kaina. 28Sai ka faɗa musu cewa, ‘Ni Ubangiji na rantse da zatina, abin da kuka sanar da ni zan yi muku. 29#Ibr 3.17Gawawwakin waɗanda suka yi gunaguni a kaina za su fādi cikin jejin nan. Dukan waɗanda aka ƙidaya, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, 30ba wanda zai shiga ƙasar da na rantse ta zama wurin zamanku, sai Kalibu, ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun. 31Amma 'yan ƙanananku, waɗanda kuka ce za su zama ganima, su ne zan kai su cikin ƙasar, za su san ƙasar da kuka raina. 32Amma ku, gawawwakinku za su fāɗi a jejin. 33#A.M 7.36'Ya'yanku za su yi yawo a jeji shekara arba'in, za su sha wahala saboda rashin bangaskiyarku, har mutuminku na ƙarshe ya mutu a jejin. 34Bisa ga kwanakin nan arba'in da kuka leƙi asirin ƙasar, haka za ku ɗauki alhakin zunubanku shekara arba'in, gama kowane kwana a maimakon shekara yake. Ta haka za ku sani ban ji daɗin abin da kuka yi ba. 35Ni Ubangiji na faɗa, hakika, haka zan yi da wannan mugun taron jama'ar da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su ƙare ƙaƙaf a wannan jeji, a nan za su mutu.’ ”
36Mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama'a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, 37mutanen nan da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta kashe su a gaban Ubangiji. 38Sai dai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne, kaɗai ne ba za su mutu ba daga cikin waɗanda suka tafi leƙen asirin ƙasar.
Ƙoƙarin Cin Ƙasar na Farko ya Kāsa
(M.Sh 1.41-46)
39Da Musa ya faɗa wa Isra'ilawa abin da Ubangiji ya ce, sai jama'a suka yi baƙin ciki ƙwarai. 40Suka tashi da sassafe, suka hau kan tudu, suna cewa, “Ga shi, a shirye muke mu tafi wurin da Ubangiji ya ambata, gama mun yi kuskure.”
41Amma Musa ya ce, “Me ya sa kuke karya umarnin Ubangiji? Yin haka ba zai kawo nasara ba. 42Kada ku haura domin kada ku sha ɗibga a gaban maƙiyanku, gama Ubangiji ba ya tare da ku. 43Gama akwai Amalekawa da Kan'aniyawa a gabanku, za su kashe ku da takobi domin kun bar bin Ubangiji, don haka Ubangiji ba zai kasance tare da ku ba.”
44Amma sai suka yi izgili, suka haura kan tudun, amma akwatin alkawari da Musa ba su bar zangon ba. 45Sai Amalekawa da Kan'aniyawa, mazauna a kan tudun, suka gangaro, suka ci su, suka runtume su har Harma, wato hallakarwa.
Currently Selected:
L.Ƙid 14: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979