Josh 1
1
Shirin da Aka Yi don Cin Ƙasar Kan'ana
1Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki, 2“Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'an nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra'ilawa. 3#M.Sh 11.24,25 Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku, kamar yadda na alkawarta wa Musa. 4Tun daga jejin, da Lebanon, har zuwa babban kogin, wato Kogin Yufiretis, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum wajen yamma, za ta zama ƙasarku. 5#M.Sh 31.6,8; Ibr 13.5 Ba mutumin da zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Kamar yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai, ba zan kunyatar da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba. 6#M.Sh 31.6,7,23 Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama'a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu. 7Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da haka nan za ka arzuta cikin dukan harkokinka. 8Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara. 9Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.”
10Sai Joshuwa ya umarci shugabannin jama'a, ya ce, 11“Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ”
12 #
L.Ƙid 32.28-32; M.Sh 3.18-20; Josh 22.1-6 Joshuwa kuma ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, 13“Ku tuna da maganar da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku da ita, ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai hutar da ku, zai kuma ba ku wannan ƙasa.’ 14Da matanku, da 'yan ƙanananku, da dabbobinku, za su zauna a ƙasar da Musa ya ba ku a wannan hayin Urdun, amma jarumawanku su haye tare da 'yan'uwanku da shirin yaƙi domin su taimake su, 15har lokacin da Ubangiji ya hutar da 'yan'uwanku kamarku, su kuma su mallaki ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba su, a sa'an nan za ku koma zuwa ƙasar da take mulkinku, ku mallake ta, wato ƙasar da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun wajen gabas.”
16Su kuwa suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Iyakar abin da ka umarce mu za mu yi, duk inda ka aike mu kuma za mu tafi. 17Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya a kowane abu haka nan za mu yi maka biyayya, Ubangiji Allahnka dai ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance tare da Musa. 18Duk wanda ya ƙi bin umarninka, bai kuwa yi biyayya da maganarka da dukan irin abin da ka umarce shi ba, za a kashe shi. Kai dai ka dāge, ka yi ƙarfin hali.”
Currently Selected:
Josh 1: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979