M.Sh 34
34
Rasuwar Musa
1Sai Musa ya tashi daga filayen Mowab zuwa Dutsen Nebo, a ƙwanƙolin Fisga wanda yake daura da Yariko. Sai Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, tun daga Gileyad har zuwa Dan, 2da dukan Naftali, da ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, da dukan ƙasar Yahuza har zuwa Bahar Rum, 3da Negeb, da filin kwarin Yariko, birnin itatuwan giginya, har zuwa Zowar. 4#Far 12.7; Far 26.3; Far 28.13 Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.”
5Nan fa, a ƙasar Mowab, Musa bawan Ubangiji, ya rasu kamar yadda Ubangiji ya faɗa. 6Aka binne shi cikin kwarin ƙasar Mowab, kusa da Betfeyor, amma ba wanda ya san inda aka binne shi har yau. 7Musa ya yi shekara ɗari da ashirin sa'ad da ya rasu. Idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuma bai ragu ba. 8Isra'ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab har kwana talatin. Sa'an nan kwanakin kuka da makoki domin Musa suka ƙare.
9Joshuwa ɗan Nun yana cike da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya masa hannuwansa. Isra'ilawa suka yi masa biyayya, suka aikata bisa ga yadda Ubangiji ya umarci Musa.
10 #
Fit 33.11
Tun daga lokacin nan, ba a taɓa yin wani annabi a Isra'ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska. 11Ubangiji ya aike shi ya aikata alamu da mu'ujizai a ƙasar Masar a gaban Fir'auna da dukan barorinsa, da dukan ƙasarsa. 12Ya kuma aikata ayyuka masu iko, masu bantsoro a gaban dukan Isra'ilawa.
Currently Selected:
M.Sh 34: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979