Ayu 40
40
1Ubangiji ya yi wa Ayuba magana.
2“Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka?
Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.”
3Ayuba ya amsa wa Ubangiji ya ce,
4“Ai, ni ba a bakin kome nake ba,
Wace amsa zan ba ka?
Na rufe bakina na yi gam.
5Ai, na riga na yi magana sau ɗaya, har ma sau biyu,
Ba zan amsa ba, ba zan ƙara cewa kome ba.”
Bayyanuwar Ikon Allah
6Sa'an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba daga cikin guguwa, ya ce,
7“Tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,
Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.
8Kai kanka za ka sa mini laifi?
Za ka kā da ni don kai ka barata?
9Kana da ƙarfi kamar na Allah?
Kana iya tsawa da murya kamar tasa?
10“Ka caɓa ado da kwarjini da ɗaukaka,
Ka yafa daraja da maƙami.
11Ka kwararar da rigyawar fushinka,
Ka dubi dukan wanda yake alfarma, a wulakance.
12Ka dubi dukan wanda yake alfarma ka ƙasƙantar da shi,
Ka tattake mugaye a inda suke.
13Dukansu ka binne su a ƙasa,
Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira.
14Sa'an nan ni kaina kuma zan sanar da kai,
Cewa da hannun damanka za ka yi nasara.
15“Ga dorina wanda ni na halicce ta,
Kamar yadda na halicce ka,
Tana cin ciyawa kamar sa.
16Ga shi, ƙarfinta yana cikin ƙugunta,
Ikonta yana cikin tsakar cikinta.
17Na yi mata wutsiya miƙaƙƙiya, mai ƙarfi kamar itacen al'ul,
Jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe wuri ɗaya
18Ƙasusuwanta bututun tagulla ne,
Gaɓoɓinta kamar sandunan ƙarfe ne.
19“Ita ce ta farko cikin ayyukan Allah,
Sai Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkararta da takobi!
20Gama duwatsu suke ba ta abinci,
A inda dukan namomin jeji suke wasa.
21Takan kwanta a inuwar ƙaddaji,
Ta ɓuya a cikin iwa, da a fadama.
22Gama inuwar da take rufe ta ta ƙaddaji ce,
Itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
23Ga shi, ba ta jin tsoron tumbatsar kogi,
A natse take, ko da ta bakinta rigyawar Urdun take wucewa.
24Akwai wanda zai iya kama ta da ƙugiya,
Ko ya sa mata asirka?”
Currently Selected:
Ayu 40: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979