Ayu 39
39
1“Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa?
Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
2Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu?
Ka san lokacin haihuwarsu?
3Ka san lokacin naƙudarsu, sa'ad da suke haihuwar 'ya'yansu,
Lokacin da 'ya'yansu suke fita cikinsu?
4'Ya'yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura,
Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu.
5“Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so?
Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri,
6Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa,
Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa?
7Yakan yi wa hayaniyar birane ba'a,
Ba ruwansa da tsawar masu kora.
8Tsaunukan duwatsu ne wurin kiwonsa,
A can yake neman kowane ɗanyen abu.
9“Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki?
Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka?
10Ka iya ɗaure shi da igiya a kwarin kunya?
Ko kuwa zai yi maka kaftu a fadamarka?
11Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa?
Za ka kuma bar masa aikinka?
12Ka gaskata zai komo,
Ya kawo maka hatsi a masussukarka?
13“Jimina takan karkaɗa fikafikanta da alfarma!
Amma ba su ne gashin fikafikan ƙauna ba.
14Jimina takan bar wa ƙasa ƙwayayenta,
Ta bar ƙasa ta ɗumama su.
15Takan manta wani ya iya taka su su fashe,
Ya yiwu kuma wani naman jeji ya tattake su.
16Takan yi wa 'ya'yanta mugunta,
Sai ka ce ba nata ba ne,
Ko da yake ta sha wahala a banza,
Duk da haka ba ta damu ba.
17Gama Allah bai ba ta hikima ba,
Bai kuwa ba ta fahimi ba.
18Amma sa'ad da ta sheƙa a guje,
Takan yi wa doki maguji da mahayinsa dariya.
19“Kai ka yi wa doki ƙarfinsa?
Kai ne kuma ka daje wuyansa da geza?
20Kai ne ka sa shi tsalle kamar ɗango?
Kwarjinin firjinsa yana da bantsoro.
21Yakan yi nishi a fadama,
Yana murna saboda ƙarfinsa,
A wurin yaƙi ba ya ja da baya, ba ya jin tsoron kibau.
22Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba.
Ba ya ba da baya ga takobi,
23Kibau na ta shillo a kansa,
Māsu suna ta gilmawa a gabansa.
24Da tsananin fushi da hasala yana kartar ƙasa,
Da jin ƙarar ƙaho, sai ya yi ta zabura.
25Sa'ad da aka busa ƙaho yana ce, ‘Madalla.’
Yakan ji warin yaƙi daga nesa, da hargowar sarakunan yaƙi da ihunsu.
26“Ta wurin hikimarka ne shirwa take tashi,
Ta buɗe fikafikanta ta nufi kudu?
27Ta wurin umarninka ne gaggafa take tashi sama
Ta yi sheƙarta can ƙwanƙoli?
28A kan dutse take zaune, a can take gidanta,
Cikin ruƙuƙin duwatsu.
29Daga can takan tsinkayi abincinta
Idanunta sukan hango shi tun daga nesa.
30 #
Mat 24.28; Luk 17.37 'Yayanta sukan tsotsi jini,
A inda kisassu suke, can take.”
Currently Selected:
Ayu 39: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979