Bible App logo
Search Icon

Ayu 37

37
1“Saboda wannan zuciyata takan kaɗu,
Kamar ta yi tsalle daga inda take.
2Ku kasa kunne ga tsawar muryarsa,
Ku saurara ga maganarsa mai ƙarfi.
3Yakan sako ta a ƙarƙashin samaniya duka,
Walƙiyarsa takan zagaya dukan kusurwoyin duniya.
4Bayan walƙiyar akan ji rugugin muryarsa,
Ya yi tsawa da muryarsa ta ɗaukaka,
Ko da yake an ji muryarsa bai dakatar da tsawar ba.
5Muryar tsawar Allah mai banmamaki ce,
Yana aikata manyan abubuwa da suka fi ƙarfin ganewarmu.
6Yakan umarci dusar ƙanƙara ta fāɗo bisa duniya,
Yayyafi da ruwan sama kuwa su yi ƙarfi.
7Yakan tsai da kowane mutum daga aikinsa,
Domin dukan mutane su san aikinsa.
8Namomin jeji sukan shiga wurin kwanciyarsu,
Su yi zamansu a ciki.
9Guguwa takan taso daga inda take,
Sanyi kuma daga cikin iska mai hurawa.
10Numfashin Allah yakan sa ƙanƙara,
Yakan sa manyan ruwaye su daskare farat ɗaya.
11Yakan cika girgije mai duhu da ruwa,
Gizagizai sukan baza walƙiyarsa.
12Sukan yi ta kewayawa ta yadda ya bishe su,
Don su cika dukan abin da ya umarce su a duniya da ake zaune a ciki.
13Allah yakan aiko da ruwan sama ya shayar da duniya,
Saboda tsautawa, ko saboda ƙasa, ko saboda ƙauna.
14“Ka ji wannan, ya Ayuba,
Tsaya ka tuna da ayyukan Allah masu banmamaki.
15Koka san yadda Allah yakan ba su umarni,
Ya sa walƙiyar girgijensa ta haskaka?
16Ko kuma ka san yadda gizagizai suke tsaye daram a sararin sama?
Ayyukan banmamaki na Allah, cikakken masani!
17Ko ka san abin da yake sa ka jin gumi
Sa'ad da iskar kudu take hurowa?
18Ka iya yin yadda ya yi,
Kamar yadda ya shimfiɗa sararin sama daram,
Kamar narkakken madubi?
19Ka koya mana abin da za mu faɗa masa,
Ba za mu iya gabatar da ƙararrakinmu ba, gama mu dolaye ne.
20A iya faɗa masa, cewa zan yi magana?
Mutum ya taɓa so a haɗiye shi da rai?
21“A yanzu dai mutane ba su iya duban haske,
Sa'ad da yake haskakawa a sararin sama,
Bayan da iska ta hura ta share gizagizai sarai.
22Daga arewa wani haske kamar na zinariya ya fito mai banmamaki,
Allah yana saye da ɗaukaka mai bantsoro.
23Mai Iko Dukka, ya fi ƙarfin ganewarmu,
Shi mai girma ne, da iko, da gaskiya,
Da yalwataccen adalci,
Ba ya garari.
24Saboda haka mutane suke tsoronsa,
Bai kula da waɗanda suke ɗaukar kansu su masu hikima ba ne.”

Currently Selected:

Ayu 37: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in