Bible App logo
Search Icon

Ayu 34

34
Elihu ya ga Allah ya yi Daidai
1Elihu ya ci gaba.
2“Ku mutane masu hikima, ku ji maganata,
Ku kasa kunne ga abin da zan faɗa, ku masana.
3Kunne yake rarrabewa da magana,
Kamar yadda harshe yake rarrabewa da ɗanɗanar abinci.
4Bari mu zaɓi abin da yake daidai,
Bari kuma mu daidaita abin da yake mai kyau tsakanin junanmu.
5Gama Ayuba ya ce, ‘Ni marar laifi ne,
Amma Allah ya ƙwace mini halaliyata.
6Duk da rashin laifina an ɗauke ni a maƙaryaci,
Raunina ba ya warkuwa ko da yake ba ni da laifin kome.’
7“Wane irin mutum ne kai, Ayuba,
Da kake shan raini kamar yadda kake shan ruwa,
8Wanda yake cuɗanya da ƙungiyar masu aikata laifi,
Kana yawo tare da mugaye?
9Gama ka ce, ‘Bai amfana wa mutum kome ba
Ya yi murna da Allah.’
10“Saboda haka ku kasa kunne gare ni, ku da kuke haziƙai,
Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne,
A wurin Mai Iko Dukka ba kuskure,
11 # Zab 62.12 Gama bisa ga aikin mutum yake sāka masa,
Yana sa aniyarsa ta bi shi.
12Gaskiya ce, Allah ba zai aikata mugunta ba,
Mai Iko Dukka ba zai kauce wa adalci ba.
13Wa ya shugabantar da shi a kan duniya?
Wa ya mallakar masa da duniya duka?
14Da zai amshe ruhu da numfashin da ya hura wa mutum,
15Da duk mai rai ya halaka,
Mutum kuma ya koma ƙura.
16“Idan kai haziƙi ne, to, ji wannan,
Kasa kunne ga abin da zan faɗa.
17Da Allah maƙiyin adalci ne, da ya yi mallaka?
Ka iya sa wa Adali, Mai Iko Dukka laifi?
18Ka iya sa wa Allah laifi,
Shi da ya ce, ‘Sarki marar amfani ne,
Hakimai kuma mugaye’?
19Ba ya nuna sonkai ga sarakuna,
Ko kuma ya fi kulawa da attajira fiye da matalauta,
Gama shi ya halicce su duka.
20Sukan mutu nan da nan,
Da tsakar dare manya da ƙanana sukan shuɗe farat ɗaya,
An kawar da su ba da hannun mutum ba.
21“Gama yana ganin al'amuran mutum,
Yana kuma ganin dukan manufarsa.
22Ba wani duhu, ko duhu baƙi ƙirin
Inda masu aikata mugunta za su ɓuya.
23Ba ajiyayyen lokacin da ya ajiye wa kowane mutum
Da zai je shari'a a gaban Allah.
24Yakan ragargaza ƙarfafa ba tare da wani bincike ba,
Ya sa waɗansu a madadinsu.
25Saboda sanin ayyukansu,
Yakan kaɓantar da su da dare ya ragargaza su,
26Yakan buge su a gaban mutane saboda muguntarsu,
27Don sun daina binsa, ba su kula da ko ɗaya
Daga cikin umarnansa ba.
28Suka sa matalauta su yi kuka ga Allah,
Ya kuwa ji kukan waɗanda ake tsananta wa.
29Idan Allah zai yi shiru, da wa zai sa wa wani laifi?
Idan ya ɓoye fuskarsa, wa zai iya ganinsa,
Ko aka yi wa al'umma ko ga mutum?
30Bai kamata marar tsoron Allah ya yi mulki ba,
Don kada ya tura jama'a cikin tarko.
31“Akwai wanda zai ce wa Allah, ‘Ni horarre ne,
Ba zan ƙara yin laifi ba?
32Ka koya mini abin da ban sani ba,
Idan na yi laifi, ba zan ƙara yi ba.’
33Zai kuɓutar domin ya gamshe ka saboda ka ƙi yarda?
Tilas kai za ka zaɓa, ba ni ba,
Saboda haka sai ka hurta abin da ka sani.
34“Haziƙan mutane da mutum mai hikima da suka ji ni za su ce,
35‘Ayuba yakan yi magana ne ba tare da sanin abin da yake yi ba,
Maganarsa ba ta mai hangen nesa ba ce.
36Da ma a gwada Ayuba har ƙarshe,
Saboda amsar da yake bayarwa ta mugaye.
37Gama ya ƙara zunubinsa da tayarwa,
Yana tafa hannunsa a tsakaninmu,
Yana yawaita maganganunsa gāba da Allah.’ ”

Currently Selected:

Ayu 34: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in