Bible App logo
Search Icon

Ayu 33

33
Elihu Ya Tsauta wa Ayuba
1“Amma yanzu, kai Ayuba, ka yarda ka ji maganata,
Ka kasa kunne ga dukan abin da zan faɗa.
2Ga shi, na buɗe baki in yi magana.
3Maganar da zan hurta ainihin gaskiyar da take a zuciyata ce,
Abin da zan faɗa kuma dahir ne.
4Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.
5“Ka amsa mini, in ka iya,
Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.
6Duba, ni da kai ɗaya muke a wajen Allah,
Dukanmu biyu kuma daga yumɓu aka siffata mu.
7Don haka kada ka razana saboda ni,
Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.
8“Hakika na ji maganar da ka yi,
Na kuwa ji amon maganganunka,
9Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi,
Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.
10Ka ce Allah ya zarge ka ya ɗauke ka tankar maƙiyansa,
11 # Ayu 13.27 Ya saka ka a turu,
Yana duban dukan al'amuranka.
12“Amma a kan wannan, Ayuba, ka yi kuskure, zan ba ka amsa,
Gama Allah ya fi kowane mutum girma.
13Me ya sa kake yi wa Allah gunaguni,
Cewa ba ya karɓar maganarka ko ɗaya?
14Gama Allah yakan yi magana sau ɗaya ne,
I, har sau biyu, duk da haka mutum ba ya lura.
15 # Ayu 4.13 Yakan sanar a mafarkai ko a wahayi
Sa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su,
A sa'ad da suke barci a gadajensu.
16Yakan buɗe kunnuwan mutane,
Ya tsorata su da faɗakarwarsa,
17Domin ya kawar da su daga aikin da suke yi,
Ya kuma kawar musu da girmankai.
18Yakan hana su zuwa kabari,
Ya hana ransu halaka da takobi.
19“Akan hori mutum da cuta mai zafi a gadonsa,
Ya yi ta fama da azaba a cikin ƙasusuwansa,
20Ransa yana ƙyamar abinci,
Yana ƙyamarsa kome daɗinsa kuwa.
21Yakan rame ƙangayau, ƙasusuwansa duk a waje.
22Yana gab da shiga kabari,
Ransa yana hannun mala'ikun mutuwa.
23“Da a ce akwai wani mala'ika mai sulhuntawa a tsakani,
Ko da ɗaya daga cikin dubu ne wanda zai faɗa wa mutum,
24Mala'ikan da zai yi masa alheri ya ce,
‘Ka cece shi daga gangarawa zuwa cikin kabari,
Na sami abin da zai fanshe shi!’
25Naman jikinsa zai koma kamar na saurayi,
Zai komo kamar lokacin da yake gaɓar ƙarfinsa.
26Sa'an nan ne mutum zai yi addu'a ga Allah, ya karɓe shi,
Ya zo gabansa da murna,
Allah zai komar wa mutum da adalcinsa.
27Zai raira waƙa a gaban jama'a, ya ce, ‘Na yi zunubi. Ban yi daidai ba,
Amma ba a sa ni in biya ba.
28Allah ya fanshe ni daga gangarawa zuwa kabari,
Raina kuwa zai ga haske.’
29“Ga shi kuwa, Allah ya yi dukan waɗannan abubuwa sau biyu, har ma sau uku ga mutum,
30Don ya komo da ran mutum daga kabari,
Domin a haskaka shi da hasken rai.
31“Haba Ayuba, ka kula fa, ka kasa kunne,
Ga abin da nake faɗa,
Ka yi shiru, zan yi magana.
32Amma idan kana da ta cewa, to, amsa,
Yi magana, gama ina so in kuɓutar da kai.
33In kuwa ba haka ba, sai ka yi shiru,
Ka kasa kunne gare ni,
Zan kuwa koya maka hikima.”

Currently Selected:

Ayu 33: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in