YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 21

21
Ayuba Ya Yi Magana a kan Wadatar Mugaye
1Ayuba ya amsa.
2“Ku kasa kunne ga abin da nake faɗa,
Wannan ita ce ta'aziyyar da nake nema a gare ku.
3Ku ba ni zarafi in yi magana, sa'an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.
4“Ba da 'yan adam nake faɗa ba,
Ina da isasshen hanzarin da zai sa in yi fushi.
5Ku dube ni, ashe, wannan bai isa ya sa ku yi zuru,
Ku firgita, ku yi shiru ba?
6Sa'ad da na tuna da abin da ya same ni,
Sai jikina ya yi suwu, in yi ta makyarkyata ina rawar jiki.
7Me ya sa Allah yake barin mugaye
Har su tsufa su kuma yi arziki?
8'Ya'yansu da jikokinsu sukan girma a idonsu.
9Allah bai taɓa aukar wa gidajensu da bala'i ba,
Ba su taɓa zama a razane ba.
10Hakika shanunsu suna ta hayayyafa,
Suna haihuwa ba wahala.
11'Ya'yansu suna guje-guje,
Suna tsalle kamar 'yan raguna,
12Suna rawa ana kaɗa garaya,
Ana busa sarewa.
13Suka yi zamansu da salama,
Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.
14Mugaye sukan ce wa Allah ya ƙyale su kurum,
Ba su so su san nufinsa game da hanyoyinsu.
15Suna tsammani ba amfani a bauta wa Allah,
Ko a yi addu'a gare shi domin samun wata fa'ida.
16Sukan ce ta wurin ƙarfinsu ne suka yi nasara,
Amma ban yarda da irin tunaninsu ba.
17“An taɓa kashe hasken mugun mutum?
Ko masifa ta taɓa fāɗa wa wani daga cikinsu?
Allah ya taɓa hukunta wa mugu da fushi,
18Ya kuma sa su zama kamar tattakar da iska yake kwashewa?
Ko kuma kamar ƙura wadda hadiri yake kwashewa?
19“Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa.
A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi.
Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.
20Bari dai a hukunta masu zunubi
Su kuma ga hasalar Allah.
21Bayan rasuwar mutum,
Ruwansa ne ya sani ko 'ya'yansa suna jin daɗi?
22Mutum zai iya koya wa Allah?
Mutum zai iya shara'anta wa Allah Mai Iko Dukka?
23“Waɗansu mutane sukan yi zamansu ba ciwon kome har ranar mutuwarsu,
Suna cikin farin ciki da jin daɗi,
24Jikunansu kuwa sun yi ɓulɓul.
25Waɗansu kuwa ba su taɓa sanin farin ciki ba.
Sukan yi dukan kwanakinsu su mutu da baƙin ciki.
26Amma duk abu guda ne su, mutuwa za su yi, a binne,
Tsutsotsi su lulluɓe su duka.
27“Na san irin tunaninku na hassada,
28Kuna ta tambaya, ‘Ina ne gidan babban mutumin nan yanzu,
Wato mutumin da yake aikata mugunta?’
29“Ashe, ba ku yi magana da matafiya ba?
Ba ku kuma san rahoton da suka kawo ba?
30A ranar da Allah ya yi fushi, ya yi hukunci,
A kullum mugun ne kaɗai yakan kuɓuta.
31Ba wanda zai fito fili ya zargi mugun,
Ko ya mayar masa da martani.
32Sa'ad da aka ɗauke shi zuwa hurumi,
A inda ake tsaron kabarinsa,
33Dubban mutane sukan tafi wurin jana'izarsa,
Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali.
34“Amma ku, ƙoƙari kuke yi ku ta'azantar da ni da maganganun banza.
Duk abinda kuka faɗa ƙarya ne!”

Currently Selected:

Ayu 21: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in