YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 20

20
Zofar Ya Nuna Rabon Mugu
1Zofar ya amsa.
2“Ayuba, ka ɓata mini rai,
Ba zan yi haƙuri ba, sai na ba ka amsa.
3Abin da ka faɗa raini ne,
Amma na san yadda zan ba ka amsa.
4“Hakika ka sani tun daga zamanin dā,
Sa'ad da aka fara sa mutum a duniya,
5Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.
6Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama.
Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.
7Amma zai shuɗe kamar ƙura.
Waɗanda dā suka san shi,
Za su yi mamaki saboda rashin sanin inda ya tafi.
8Zai ɓace kamar mafarki, kamar wahayi da dad dare,
Ba kuwa za a ƙara ganinsa ba.
9Ba za a ƙara ganinsa a wurin zamansa ba.
10Tilas 'ya'yansa maza su biya zambar da ya yi wa matalauta,
Tilas hannuwansa su biya dukiyar da ya ƙwace.
11Ko da yake gagau yake, ma'aikaci ne kuma sa'ad da yake yaro,
Duk da haka ba da jimawa ba, zai zama ƙura.
12-13Ɗanɗana mugunta yana da daɗi a gare shi ƙwarai,
Yakan sa wata a bakinsa don ya riƙa jin daɗin tsotsanta.
14Amma a cikinsa wannan abinci yakan zama da ɗaci,
Ɗacinsa kamar na kowane irin dafi mai ɗaci ne.
15Mugun mutum yakan harar da dukiyar da ya samu ta hanyar zamba,
Allah zai karɓe ta har da wadda ya ci a cikin cikinsa.
16Abin da mugu ya haɗiye kamar dafi yake,
Yakan kashe shi kamar saran maciji mai mugu dafi.
17Zai mutu bai ga kogunan man zaitun ba,
Ba kuwa zai ga rafuffukan da suke da yalwar albarka ba.
18Tilas ya rabu da dukan abin da ya yi wahalarsa.
Ba dama ya mori dukiyarsa,
19Saboda zalunci da rashin kula da matalauta,
Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.
20“Har abada ba zai kai ga samun abin da yake wahala ba.
21Sa'ad da ya ci ba zai yi saura ba,
Gama yanzu dukiyarsa ta ƙare.
22A lokacin da yake gaɓar samunsa,
Baƙin ciki mai nauyin gaske zai ragargaza shi.
23Bari ya ci duk irin abin da yake so!
Allah zai hukunta shi da hasala da fushi.
24Lokacin da yake ƙoƙari ya kuɓuta daga takobin baƙin ƙarfe,
Za a harbe shi da bakan tagulla ya fāɗi warwar.
25Kibiya za ta kafe a jikinsa
Tsininta zai yi ta ɗiɗɗiga da jini,
Razana ta kama zuciyarsa.
26Aka hallaka dukan abin da ya tattara,
Wutar da ba hannun mutum ya kunna ba
Ta ƙone shi, shi da iyalinsa duka.
27Samaniya ta bayyana zunubin wannan mutum,
Duniya kuma ta ba da shaida gāba da shi.
28Dukan dukiyarsa za a hallaka ta a rigyawar fushin Allah.
29“Wannan ita ce ƙaddarar mugaye,
Wadda Allah ya ƙayyade musu.”

Currently Selected:

Ayu 20: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in