YouVersion Logo
Search Icon

Irm 6

6
Ajalin Urushalima da Yahuza
1“Ya ku mutanen Biliyaminu, ku
gudu neman mafaka,
Daga cikin Urushalima!
Ku busa ƙaho a Tekowa,
Ku ba da alama a Bet-akkerem,
Gama masifa da babbar halaka sun
fito daga arewa.
2Ya Sihiyona, ke kyakkyawar
makiyaya ce, zan hallaka abin da
kika hahhaifa.
3Makiyaya da garkunansu za su zo
wurinki,
Za su kafa alfarwansu kewaye da ke,
Kowa zai yi kiwo a makiyayarki.
4Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa mata
da yaƙi!
Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakar
rana!’
Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, ga
rana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi.
5Mu tashi mu fāɗa mata da dare,
Mu lalatar da fādodinta.’ ”
6Ubangiji Mai Runduna ya ce,
“Ku sassare itatuwanta,
Ku tula ƙasa kewaye da
Urushalima,
Dole in hukunta wannan birni
saboda ba kome cikinsa sai
zalunci,
7Kamar yadda rijiya take da ruwa
garau,
Haka Urushalima take da
muguntarta,
Ana jin labarin kama-karya da na
hallakarwa a cikinta,
Kullum akwai cuce-cuce, da raunuka
a gabana,
8Ku ji faɗaka, ya ku mutanen
Urushalima,
Don kada a raba ni da ku,
Don kada in maishe ku kufai,
Ƙasar da ba mazauna ciki.”
9Ubangiji Mai Runduna ya ce,
“Za a kalace ringin Isra'ila sarai,
kamar yadda ake wa inabi,
Ka miƙa hannunka a kan rassanta
kamar mai tsinkar 'ya'yan
inabi.”
10Da wa zan yi magana don in faɗakar
da shi, don su ji?
Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, su
ji,
Ga shi, maganar Ubangiji kuwa ta
zama abin ba'a a gare su,
Ba su marmarinta.
11-12Don haka ina cike da fushin
Ubangiji
Na gaji da kannewa.
Ubangiji ya ce,
“Zan kwararo fushi kan yara da suke a
titi.
Da kuma kan tattaruwar samari.
Za a ɗauke mata da miji duka biyu,
Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa
tukub-tukub.
Za a ba waɗansu gidajensu, da
gonakinsu, da matansu,
Gama zan nuna ikona in hukunta
mazaunan ƙasar.
13Gama daga ƙaraminsu zuwa babba,
Kowannensu yana haɗama ya ci
ƙazamar riba,
Har annabawa da firistoci,
Kowannensu ya shiga aikata rashin
gaskiya.
14 # Eze 13.10 Sun warkar da raunin mutanena
sama sama,
Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali
kuwa ba lafiya.
15 # Irm 8.10-12 Sun ji kunya sa'ad da suka aikata
abubuwan banƙyama?
Ba su ji kunya ba ko kaɗan.
Ko gezau ba su yi ba,
Don haka za su fāɗi tare da
fāɗaɗɗu,
Sa'ad da na hukunta su, za a
hamɓarar da su.
Ni Ubangiji na faɗa.”
16Haka Ubangiji ya ce,
“Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba,
Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya
mai kyau take,
Ku bi ta, don ku hutar da
rayukanku.
Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’
17Na sa muku matsara cewa, in kun ji
an busa ƙaho ku kula!
Amma suka ce, ‘Ba za mu kula ba.’
18“Don haka, ku ji, ya ku al'ummai,
Ku sani, ku taron jama'a,
Don ku san abin da zai same ku.
19Ki ji, ya ke duniya,
Ga shi, ina kawo masifa a kan
wannan jama'a,
Sakayyar ƙulle-ƙullensu,
Don ba su kula da maganata ba,
Sun ƙi dokokina.
20Da wane nufi kuke kawo mini turare
daga Sheba,
Ko raken da kuke kawowa daga
ƙasa mai nisa?
Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa
ba,
Ba kuwa zan ji daɗin sadakokinku
ba.
21Don haka, ni Ubangiji na ce,
Zan sa abin tuntuɓe a gaban wannan
jama'a,
Za su kuwa yi tuntuɓe, su fāɗi.
Iyaye tare da 'ya'yansu, da
maƙwabci,
Do abokansu za su lalace.”
22Haka Ubangiji ya ce,
“Ga shi, jama'a tana fitowa daga
ƙasar arewa.
Babbar al'umma ce,
Ta yunƙuro tun daga manisantan
wurare na duniya.
23Suna riƙe da baka da māshi,
Mugaye ne marasa tausayi,
Motsinsu kamar ƙugin teku ne.
Suna haye a kan dawakai,
A jere kamar wanda ya yi shirin
yaƙi
Gāba da ke, ya 'yar Sihiyona.”
24Mutanen Urushalima sun ce,
“Mun ji labarin yaƙin,
Hannuwanmu suka yi rauni.
Azaba ta kama mu,
Ciwo irin na mai naƙuda.
25Kada ku fita zuwa gona,
Kada kuma ku yi yawo a kan
hanya,
Gama abokin gāba yana da takobi,
Razana a kowane sashi.”
26“Ya mutanena, ku sa tufafin makoki,
Ku yi birgima cikin toka,
Ku yi makoki mai zafi irin wanda
akan yi wa ɗa tilo,
Gama mai hallakarwa zai auko mana
nan da nan.”
27Ubangiji ya ce wa Irmiya,
“Na maishe ka mai aunawa da mai
jarraba mutanena
Domin ka sani, ka auna
al'amuransu,
28Su duka masu taurinkai ne, 'yan
tawaye,
Suna yawo suna baza jita-jita.
Su tagulla ne da baƙin ƙarfe,
Dukansu lalatattu ne.
29Ana zuga da ƙarfi,
Dalma ta ƙone,
Tacewar aikin banza ne,
Gama ba a fitar da mugaye ba.
30Ana ce da su ƙwan maƙerar azurfa
ne,
Gama ni na ƙi su.”

Currently Selected:

Irm 6: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in