YouVersion Logo
Search Icon

Irm 5

5
Zunubin Urushalima da Yahuza
1“Ku bi titunan Urushalima ko'ina!
Ku dudduba ku lura!
Ku bincika kowane dandali, ku gani,
Ko za ku iya samun ko mutum ɗaya
Mai aikata adalci, mai son gaskiya,
Sai in gafarta mata.
2Ko da yake suna cewa, ‘Na rantse da
ran Ubangiji,’
Duk da haka rantsuwar ƙarya suke
yi.”
3Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya
kake so ba?
Ka buge su, amma ba su yi nishi ba,
Ka hore su, amma sun ƙi horuwa,
Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse,
Sun ƙi tuba.
4Sai na ce,
“Waɗannan mutane ba su da kirki,
Ba su da hankali,
Ba su san hanyar Ubangiji,
Ko shari'ar Allahnsu ba.
5Zan tafi wurin manyan mutane, in yi
musu magana,
Gama sun san nufin Ubangiji, da
shari'ar Allahnsu.”
Amma dukansu sun ƙi yarda
Ubangiji ya mallake su,
Suka ƙi yi masa biyayya.
6Domin haka zaki daga kurmi zai
kashe su,
Kyarkeci kuma daga hamada zai
hallaka su.
Damisa tana yi wa biranensu
kwanto,
Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a
yayyage shi,
Domin laifofinsu sun yi yawa,
Karkacewarsu babba ce.
7“Don me zan gafarce ki?
'Ya'yanki sun rabu da ni,
Sun yi rantsuwa da gumaka,
Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai,
Suka yi karuwanci, suka ɗunguma
zuwa gidajen karuwai,
8Kamar ƙosassun ingarmu suke,
masu jaraba,
Kowa yana haniniya, yana neman
matar maƙwabcinsa.
9Ba zan hore su saboda waɗannan
abubuwa ba?
Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wa
kaina fansa a kan wannan
al'umma ba?
10Ku haura, ku lalatar da gonar
kurangar inabinta,
Amma kada ku yi mata ƙarƙaf,
Ku sassare rassanta,
Gama su ba na Ubangiji ba ne.
11Gama mutanen Isra'ila da mutanen
Yahuza
Sun zama marasa aminci a gare ni.
Ni Ubangiji na faɗa.”
12Sun yi ƙarya a kan Ubangiji,
Suka ce, “Ba abin da zai yi,
Ba wata masifa da za ta same mu.
Ba kuwa za mu ga takobi ko yunwa
ba.
13Annabawa holoƙo ne kawai,
Maganar ba ta cikinsu.
Haka za a yi da su!”
Urushalima tana gab da Faɗuwa
14Saboda haka Ubangiji Allah Mai
Runduna ya ce,
“Domin sun hurta wannan magana,
Ga shi, zan sa maganata a bakinka ta
zama wuta,
Waɗannan mutane kuwa su zama
itace,
Wutar za ta cinye su.
15“Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, ina
kawo muku
Wata al'umma daga nesa,” in ji
Ubangiji,
“Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tun
zamanin dā.
Al'umma wadda ba ku san harshenta
ba,
Ba za ku fahimci abin da suke faɗa
ba.
16Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari
ne,
Dukansu jarumawa ne.
17Za su cinye amfanin gonakinku da
abincinku.
Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza.
Za su cinye garkunanku na tumaki,
da na awaki, da na shanu,
Za su kuma cinye 'ya'yan inabinku
da na ɓaurenku.
Za su hallaka biranenku masu kagara
da takobi, waɗanda kuke fariya da
su.
18“Amma ko a cikin waɗancan kwanaki ba zan yi muku ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji. 19“Sa'ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ Sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”
20“Ka sanar wa zuriyar Yakubu da
wannan,
Ka kuma yi shelarsa a Yahuza, ka
ce,
21 # Ish 6.9,10; Eze 12.2; Mar 8.18 ‘Ku ji wannan, ya ku wawaye,
marasa hankali,
Kuna da idanu, amma ba ku gani,
Kuna da kunnuwa, amma ba ku
ji.’ ”
22 # Ayu 38.8-11 Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona
ba?
Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba?
Ni ne na sa yashi ya zama iyakar
teku,
Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta
hayuwa,
Ko da yake raƙuman ruwa za su yi
hauka, ba za su iya haye ta ba,
Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta
ba.
23Amma mutanen nan suna da taurin
zuciya, masu halin tayarwa ne,
Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.
24A zuciya ba su cewa,
‘Bari mu ji tsoron Ubangiji
Allahnmu
Wanda yake ba mu ruwan sama a
kan kari,
Na kaka da na bazara,
Wanda yake ba mu lokacin girbi.’
25Laifofinku sun raba ku da waɗannan
abubuwa.
Zunubanku kuma sun hana ku
samun alheri.
26“Gama an sami mugaye, a cikin
jama'ata,
Suna kwanto kamar masu kafa
ashibta.
Sun ɗana tarko su kama mutane.
27Kamar kwando cike da tsuntsaye,
Haka nan gidajensu suke cike da cin
amana,
Don haka suka zama manya, suka
sami dukiya.
28Sun yi ƙiba, sun yi bul-bul,
Ba su da haram a kan aikata
mugunta,
Ba su yi wa marayu shari'ar adalci,
don kada su taimake su.
A wajen shari'a ba su bin hakkin
matalauta.
29“Ba zan hukunta su saboda
waɗannan abubuwa ba?
Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan
al'umma irin wannan ba?
30“Abin banmamaki da bantsoro
Ya faru a ƙasar.
31Annabawa sun yi annabcin ƙarya,
Firistoci kuma sun yi mulki da ikon
kansu,
Mutanena kuwa suna so haka!
Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za
ku yi?”

Currently Selected:

Irm 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in