YouVersion Logo
Search Icon

Ish 8

8
Sunan Ɗan Annabi
1Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki allo babba ka rubuta a kansa da manyan harufa, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’ 2Nemo mutum biyu amintattu, wato Uriya firist, da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama shaidu.”
3Bayan wannan na yi jima'i da matata annabiya. Ta ɗauki ciki, ta haifi ɗa namiji, Ubangiji ya ce mini, “Ka raɗa masa suna, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’ 4Kafin yaron ya isa kiran mama ko baba, Sarkin Assuriya zai kwashe dukan dukiyar Dimashƙu da dukan ganimar Samariya.”
Sarkin Assuriya Yana Zuwa
5Ubangiji kuma ya sāke yi mini magana. 6Ya ce, “Saboda wannan jama'a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa, suka yi ta rawar jiki a gaban sarki Rezin da sarki Feka, 7ni Ubangiji kuwa, zan kawo Sarkin Assuriya da dukan sojojinsa su fāɗa wa Yahuza. Za su tasar musu kamar rigyawar Kogin Yufiretis wadda ta yi ambaliya ta shafe kowace gaɓa. 8Za su sheƙa cikin ƙasar Yahuza kamar rigyawa wadda ta kai har kafaɗa, ta rufe kome da kome.”
Allah yana tare da mu! Fikafikansa a buɗe suke su tsare ƙasar.
9Ku tattaru a tsorace ya ku sauran al'umma! Ku saurara, ya ku manisantan wurare na duniya. Ku yi shirin faɗa, amma ku ji tsoro! Hakika ku yi shiri, amma ku ji tsoro! 10Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.
Ubangiji Za Ku Ji Tsoro
11Bisa ga ikonsa mai girma Ubangiji ya faɗakar da ni kada in bi hanyar da jama'ar ke bi. Ya ce, 12#1Bit 3.14,15 “Kada ka haɗa kanka da jama'a cikin ƙulle-ƙullensu, kada kuma ka ji tsoron abubuwan da su suke jin tsoro. 13Ka tuna fa, ni Ubangiji Mai Runduna, mai tsarki ne. Wajibi ne ni kaɗai za ka ji tsoro. 14#1Bit 2.8 Saboda tsananin tsarkina na zama kamar dutse wanda mutane suke tuntuɓe da shi. Na zama kamar tarko wanda zai kama jama'ar mulkokin Yahuza da Isra'ila da mutanen Urushalima. 15Da yawa za su yi tuntuɓe su faɗi. Za su faɗi, a kuwa ragargaza su. Za a kama su da tarko.”
16Almajiraina su ne za su lura, su kuma kiyaye jawabin da Allah ya ba ni. 17#Ibr 2.13 Ubangiji ya ɓoye kansa daga jama'arsa, amma ni na dogara gare shi, na kafa zuciyata a gare shi.
18 # Ibr 2.13 Ga ni tare da 'ya'yan da Ubangiji ya ba ni. Ubangiji Mai Runduna, wanda kursiyinsa a kan Dutsen Sihiyona yake, ya maishe mu rayayyen jawabi ga jama'ar Isra'ila.
19Mutane za su riƙa ce muku ku nemi shawarar 'yan bori da masu sihiri waɗanda suke shaƙe muryar, har ba a jin abin da suke faɗa. Za su ce, “Ai, ma, ya kamata mutane su nemi shawara daga aljannu, su kuma nemi shawarar matattu saboda masu rai.”
20Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”
Lokacin Wahala
21Mutane za su yi ta kai da kawowa a ko'ina cikin ƙasar, cikin matsuwa da yunwa. A yunwar da suke sha da haushin da suke ji, za su zagi sarkinsu, su kuma zagi Allahnsu. Har ma zai yiwu su ɗaga ido su dubi sararin sama, 22ko su zura wa ƙasa ido, amma ba abin da za su gani, sai wahala da duhu mai banrazana, inda za a kora su a ciki.

Currently Selected:

Ish 8: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in